Hukumar Kidaya ta Nijeriya, NPC ta musanta labarin da ake yadawa cewa za a yi tambayoyi game da addini a lokacin kidayar da za a gudanar a watan Mayu.
Ana ta yada wani sakon murya a manhajar Whatsapp da ake kira ga Musulmai da su sani cewa za a tambaye su game da addininsu a matsayin wata hanya ta rage musu yawa a kidayar da ke tafe.
Sai dai a sanarwar da daraktan watsa labarai na NPC Isiaka Yahaya ya fitar, ya ce bidiyon na bogi ne kuma ba su da wani shiri mai kama a lokacin gudanar da kidaya.
Ya tabbatar da cewa hukumar ta kidaya ba za ta yi wata tambaya da ke da alaka da addini ba.
“An dauki matakin cire batun addini da kabila daga takardar kidayar ne domin irin tsaurin da wadannan batutuwa ke da shi a Nijeriya da kuma kare kidayar daga ce-ce-ku-cen da ba shi da amfani,” in ji hukumar.
Haka kuma hukumar ta ce ta bi diddigi ta gano cewa an soma aikawa da wannan sakon ne a manhajar Whatsapp a lokacin kidayar da aka yi a Ghana a 2021.
Ta kuma ce an soma yada wannan sakon a Nijeriya a lokacin da aka yi gwajin kidaya a watan Yulin 2022.
An soma kidayar jama’a bayan samun ‘yancin kan Nijeriya ne a 1962 inda aka kididdige cewa jama’ar kasar sun kai miliyan 45.5.
Kidaya ta karshe da aka yi a kasar an yi ta ne a 2006 inda aka kididdige cewa akwai sama da mutum miliyan 140 a kasar, sa’annan a 2019 kuma hukumar ta yi hasashen cewa jama’ar kasar sun haura mutum miliyan 200.
Me ya sa addini ke tasiri a harkokin siyasar Nijeriya?
Nurudeen Dauda, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da ya suka sa addini ke tasiri a siyasar kasar akwai batun karancin fahimtar shi kansa addinin.
“Idan ka fahimci addininka na Musulunci ka san akwai alakar da ke tsakaninka da ubangiji akwai kuma alaka tsakaninka da ‘yan uwanka Musulmi sannan akwai alaka ta zamantakewa da wadanda Allah ya halicce ku a kasa daya duk da kuna da bambancin yare da addini.
“Su ma mabiya addinin Kirista suna da makamancin irin wannan tsari,” in ji Nuradeen Dauda.
Ya bayyana cewa karancin fahimtar addini ke haifar da wannan yanayi wanda hakan ke sa a murde fahimta don a cimma wani buri.
Sannan ya ce ‘yan siyasa na amfani da gibin da ake da shi na karancin fahimtar domin cimma wani buri na su ko wata manufa.
Ya kara da cewa akwai ‘yan siyasa da suke amfani da addini domin samun tausayawa ko kuma goyon bayan mabiyansa wanda hakan ke tasiri matuka a siyasa.