Ko a shekarar 2024 sai da kasar Libya ta mayar da baƙin haure 369 da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba zuwa ƙasashensu da suka haɗa da Nijeriya da Mali. / Hoto: IOM/Stylia Kampani

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karɓi ‘yan ƙasar 180 waɗanda aka mayar da su ƙasar daga Libiya.

Hukumomin Nijeriya da ke Libiya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar da ke Kula da ‘Yan Ci-rani ta Majalisar Ɗinkin Duniya IOM ne suka jagoranci mayar da ‘yan Nijeriyar.

‘Yan Nijeriyar sun samu tarba a sashen sauka da tashi na jiragen dakon kayayyaki na Murtala Mohamed da ke Legas a ranar Laraba da dare.

Waɗanda aka mayar ƙasar sun haɗa da maza 76 da mata 92, haka kuma akwai yara takwas da kuma ƙananan yara huɗu.

Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan ci-rani da ‘yan gudun hijira na cikin gida Tijjani Ahmed ya bayyana cewa hukumasu ta NCFRMI za ta taimaka wurin samar saka waɗanda aka mayar ƙasar cikin shirye-shiryen gwamnatin tarayya da dama ma na hukumar IOM ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ahmed, wanda ya samu wakilcin mai tsara shirye-shiryen hukumar na shiyyar Kudu maso Yamma, Mista Alexander Oturu, ya bayyana cewa an kai ‘yan ci-ranin sansanin hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas inda hukumar NCFRMI da IOM suka kulla yarjejeniya a tsakaninsu domin samar da matsuguni na wucin-gadi ga wadanda suka dawo kafin a ba su alawus na sufuri domin su koma gida.

Ana yawan samun irin wannan lamarin inda ‘yan ci-rani musamman daga Nijeriya da wasu ƙasashen Turai suke maƙalewa a Libiya a yunƙurinsu na tsallakawa ƙasashen Turai, lamarin da ke kaiwa har ga asarar rayuka a sahara ko a cikin teku.

Ko a shekarar 2024 sai da kasar Libya ta mayar da baƙin haure 369 da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba zuwa ƙasashensu da suka haɗa da Nijeriya da Mali.

TRT Afrika da abokan hulda