Ƙasar Habasha da Rasha sun saka hannu kan wata yarjejeniya ta shekara uku domin faɗaɗa ɓangaren fasahar nukiliya, kamar yadda Ma'aikatar Ƙere-Ƙere da Kimiyya ta Habasha ta sanar.
Yarjejeniyar ta biyo bayan amincewa da shirin farko na kimiyyar nukiliya tsakanin ƙasashen biyu a lokacin wani babban taro wanda ya samu halartar Ministan Ƙere-Ƙere da Kimiyya na Ethiopia Belete Molla da Ministan Ci-gaban Tattalin Arziƙi na Rasha Maxim Reshetnikov a ranar Alhamis.
Shirin na nukiliya zai ɗora ne kan yarjejeniyar da aka cimma a 2023 a gefen taron tattalin arziƙi na Rasha da Afirka a St. Petersburg wadda a lokacin ta mayar da hankali ne kan binciken ci gaban tashar makamashin nukiliya da kafa Cibiyar Kimiyya da Fasaha ta Nukiliya a Habasha.
Haka kuma shirin ya haɗa da tsare-tsare don haɓaka ɓangaren nukiliya na Habasha, da kuma shirya bayar da horo da rangadi ga ƙwararru a ɓangaren na nulikiya a Habashar.
Molla ya jaddada sha'awar Habasha na yin amfani da kimiyyar nukiliya don kiwon lafiya, noma da samar da makamashi.
Sauran ƙasashen Afirka
An cim ma wannan sabuwar yarjejeniya domin faɗaɗa dangantaka ta ɓangaren kasuwanci da zuba jari da ilimi da musayar kimiyya tsakanin Habasha da Rasha
Moscow na kara fadada kawancen nukiliya a fadin Afirka, yayin da Habasha ke kokarin cusa kimiyyar nukiliya a cikin tattalin arzikinta.
Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa kamfanin nukiliya na kasar Rasha ROSATOMA ya kulla irin wannan yarjejeniyoyin da kasashe da dama da suka hada da Masar da Burkina Faso da Rwanda da Nijeriya da dai sauransu.