Wani kwamiti a Jamhuriyar Nijar mai mulkin soja ya ba da shawarar miƙa mulki ga dimokuradiyya nan da aƙalla shekaru biyar bayan kammala babban taron ƙasa, in ji jami'ai.
Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2023 tare da hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum, sojojin Nijar sun ba da shawarar wa'adin shekaru uku na mika mulki ga farar hula.
Sai dai Ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta yi watsi da shawarar. Bayan rashin jituwar siyasa, Nijar da makwabtanta Mali da Burkina Faso sun yanke shawarar ficewa daga kungiyar tare da kafa kawancen kasashen Sahel.
"An sanya wa'adin mika mulki zuwa watanni 60, wanda zai iya canzawa bisa la'akari da yanayin tsaro" da wasu dalilai, kamar yadda Abdoulaye Seydou, daya daga cikin mataimakan shugaban kwamitin ya bayyana a gidan talabijin na kasar.
Za a rusa jam'iyyun siyasa
Hukumar ta kuma yanke shawarar daukaka matsayin Birgediya Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban sojan wanda shi ne shugaban masu tsaron fadar shugaban kasar Nijar kafin juyin mulkin, zuwa mukamin Janar na soja, in ji Seydou.
Shugaban hukumar Mamoudou Harouna Djingarey ya ba da wa'adin shekaru biyar kuma ya ce za a ruguza jam'iyyun siyasa, tare da sabon kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa jam'iyyun siyasa biyu zuwa biyar.
Ya kuma ce jami'an soji za su samu damar shiga da taka rawa a zabe mai zuwa.
Aikin hukumar ya hada da tuntubar wakilai sama da 700 da suka hada da lauyoyi da malamai. Amma jam’iyyun siyasa ba su shiga ba.
Shawarar ƙarshe
Za a mika rahoton kwamitin ne ga shugabannin sojojin kasar wadanda za su yanke hukunci na karshe kan lokacin mika mulki.
Dakarun mulkin Nijar dai kamar na mulkin soja a Mali da Burkina Faso sun fatattaki sojojin Faransa da na sauran kasashen Turai tare da mayar da Rasha ƙawarsu yayin da suke fafatawa da kungiyoyin 'yan ta'adda.