Ana tuhumar wani Bature da harbe wasu mata bakar fata da bai wa alade gawarsu ya ci a Afirka ta Kudu

Ana tuhumar wani Bature da harbe wasu mata bakar fata da bai wa alade gawarsu ya ci a Afirka ta Kudu

Daga baya an gano gawarwakin matan da aka kashe din inda aka gani cewa an ciyar aladu gawarwakin nasu.
Masu zanga-zangar sun taru a wajen wata kotu a Afirka ta Kudu a ranar 2 ga watan Oktoba domin neman a hukunta wani farar fata da ake zarginsa ya kashe mata bakar fata biyu ya bai wa alade namansu. Hoto: AP

Talakawa mazauna ƙauyen Afirka ta Kudu da ke arewa maso gabashin birnin Johannesburg na yawan kutsawa cikin wata gonar alade da ke kusa da su don neman abincin da aka zubar.

Amma irin wannan yawon bin bola da wasu mata bakar fata guda biyu suka saba yi, ya kai ga yi musu kisan gilla, wanda ake zargin wani farar fata mai gona da wasu abokansa biyu da yi.

Daga baya an gano gawarwakin matan da aka kashe din inda aka gani cewa an ciyar aladu gawarwakin nasu.

Maria Makgatho, mai shekaru 44, da Locadia Ndlovu, mai shekaru 35, ba su fita daga gonar da rai ba, wadda suka shige ta don tattara yogot daga tarin kayayyakin noma da aka jefar.

Ana zubar da kayayyakin noma da suka kusa lalace ne don aladu su ci.

Gawarwakin da aka cinye

Mai gonar tare da wasu ma’aikatansa biyu suna fuskantar tuhuma kan harbe matan biyu da suka yi sanadin mutuwarsu sannan suka jefar da gawarwakinsu a cikin wani kejin alade inda ‘yan sanda suka gano gawarwakin “wadanda suka rube aka kuma cinye wasu sassan jikinsu”.

Manomin da ake zargi da ma’aikatansa biyu na ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan sanda yayin da alkali a ranar 2 ga watan Oktoba ya dage sauraron belin har zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba.

Wadanda ake zargi da kisan sun jefar da gawarwakin ne a cikin kejin alade don kawar da shaida.

Afirka ta Kudu ta ga irin tsananin wariyar launin fata da tashin hankali a ƙarƙashin mulkin wariyar launin fata har zuwa 1994.

Fushin jama'a

Wannan lamari na baya-bayan nan dai ya haifar da fushin jama'a a Afirka ta Kudu da ma wajenta, lamarin da ya kawo batutuwan da suka shafi rikicin kabilanci, cin zarafi tsakanin jinsi da ci gaba da takaddamar filaye tsakanin manoma farar fata masu fataucin fata da kuma makwabtansu bakaken fata.

Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun cewa mai gonakin da mai kula da gonar—dukkaninsu farar fata—sun shirya harbin duk masu kutsawa cikin gonar.

Wani wanda ake tuhuma, bakar fata mai shekaru 45 ma’aikacin gona, shi ma yana tsare a gidan yari bisa zarginsa da taimaka wa fararen fata biyu wajen jefar da gawarwakin a cikin kejin aladun.

Mijin daya daga cikin wadanda aka kashe wanda yake tare da matan a lokacin da suka je gona ya tsira da ransa. An harbe shi sau daya amma ya yi nasarar ficewa daga gonar don kiran likita don neman taimako.

Sauyin mulkin da kasar ta yi zuwa tsarin dimokuradiyya da kuma zaben Nelson Mandela a matsayin shugaban kasar bakar fata na farko ya nuna wani muhimmin mataki na sulhuntawa, amma har yanzu dangantakar kabilanci tsakanin fararen fata da bakar fata a Afirka ta Kudu na da tsami.

Bambancin tattalin arziki

Duk da wargaza dokokin wariyar launin fata, ana ci gaba da samun rarrabuwar kawuna a fannin tattalin arziki tsakanin farar fata da bakaken fata na Afirka ta Kudu.

Fararen fata na Afirka ta Kudu, wadanda ke da karamin kaso na al'ummar kasar, na ci gaba da rike mafi yawan dukiya da filayen kasar.

Sabanin haka, 'yan Afirka ta Kudu bakaken fata sukan fuskanci matsanancin talauci, rashin aikin yi da karancin samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya. Kusan biyu a cikin kowane baƙar fata uku a Afirka ta Kudu suna rayuwa cikin talauci.

Matsakaicin adadin mutanen da ke fama da talauci a tsakanin Turawan Afirka ta Kudu kashi daya ne kawai.

Wani rahoto na baya-bayan nan ya nuna cewa kisan da wani Baturen gona ya yi wa wasu mata bakar fata, ya yi karin haske kan rarrabuwar kawuna a Afirka ta Kudu a fannin mallakar filaye.

“During apartheid, many Black people were forced from their land, and today most major commercial farms remain under white ownership,” it said, adding that many black South Africans in rural areas continue to live in poverty and scavenge for food on farms.

"A lokacin mulkin wariyar launin fata, an tilasta wa bakar fata da dama fita daga kasarsu, kuma a yau yawancin manyan gonakin kasuwanci na ci gaba da zama karkashin mallakar farar fata," in ji ta,

Ta kara da cewa yawancin bakaken fata 'yan Afirka ta Kudu a yankunan karkara na ci gaba da rayuwa cikin talauci da kuma neman abinci a gonaki.

TRT World