Dangantaka tsakanin Nijeriya da Nijar ta yi tsami ne tun bayan da sojoji suka karbe ragamar mulki a Yamai a shekarar 2023 tare da ballewa daga kungiyar ECOWAS. / Hoto: AA

Minstan Harkokin Wajen Nijar ya gayyaci jami’a mai kula da harkokin diflomasiyya a ofishin jakadancin Nijeriya da ke ƙasar domin jin ƙarin bayani inda Nijar ɗin ke zargin Nijeriya da zama wani sansani na musamman domin kawo hargitsi a ƙasar.

Ministan Harkokin Wajen Niger Bakary Yaou Sangare ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya karanto a talabijin ɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Dangantaka tsakanin Nijeriya da Nijar ta yi tsami ne tun bayan da sojoji suka karbe ragamar mulki a Yamai a shekarar 2023 tare da ballewa daga kungiyar ECOWAS.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda a halin yanzu shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, ya yi ƙoƙarin amfani da ƙarfin soji domin mayar da hamɓararren shugaban ƙasa Mohamed Bazoum a kan mulki.

Sai dai alakar ta kara zafi a cikin watan Agusta lokacin da Abuja da Yamai suka koma hadin gwiwar tsaro da aka dage tun bayan juyin mulkin.

“Duk da ƙoƙarin da muke na ƙara daidaita dangantakar da ke tsakaninmu, muna takaicin cewa Nijeriya ba ta daina zama sansanin kawo hargitsi ga Nijar ba, tare da haɗin gwiwar wasu ƙasashen waje masu ƙarfi da kuma wasu jami’an tsohuwar gwamnati, waɗanda ta ke bai wa mafaka”, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Nijar Bakary Yaou Sangare ya bayyana a wata sanarwa da ya karanto a gidan talabijin na ƙasar.

AFP