An yi garkuwa da wasu ‘yan jarida uku na kasar Habasha da ke binciken zargin hakar zinare ba bisa ka’ida ba a yankin arewa maso yammacin yankin Tigray, kamar yadda ƙungiyarsu ta sanar a ranar Lahadi.
Tigray dai ta fuskanci mummunan rikici na tsawon shekaru biyu tsakanin sojojin gwamnatin Habasha -- wadanda ke samun goyon bayan mayakan yankin da sojojin Eritiriya - da kuma kungiyar 'yan tawayen Tigray People's Liberation Front (TPLF).
Rikicin dai ya kawo karshe a shekarar 2022 amma ya jawo lalacewar yankin inda aka kashe mutum kusan 600,000, fiye da miliyan guda kuma suka rasa matsugunansu, sannan aka lalata yawancin ababen more rayuwa a yankin.
Gidan Talabijin na Tigray ya ce 'yan jaridar uku maza -- wadanda ba a bayyana sunayensu ba -- suna gundumar Asgede ne lokacin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka sace su a cikin wani yanayi da ba a sani ba.
Kafar watsa labaran da ke da alaka da kungiyar ta TPLF ta ce 'yan jaridar na gudanar da bincike kan "lalacewar muhalli, lafiya da zamantakewar al'umma na hakar zinare ba bisa ka'ida ba a yankin" biyo bayan damuwa daga mazauna yankin.
Tigray TV ta yi Allah wadai da yin garkuwar a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X, tare da laƙabin "kai tsaye hari kan 'yancin 'yan jarida".
Majiyar ta ce ana ci gaba da kokarin gano mutanen, amma ta kara da cewa "kokarin farko na kai rahoto ga hukumomin yankin bai yi nasara ba."
"Muna fargaba kan cewa iyalansu za su shiga damuwa," in ji Abel Tsgabu, wani dan jaridar Tigray TV, a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
A shekara ta 2024, Habasha ce ta 141 a duniya wajen 'yancin 'yan jarida, a cewar kungiyar masu sa ido kan yada labarai ta Reporters Without Borders.