Bello Matawalle ya sha kakkausan suka a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara sakamakon tabarbarewar tsaro a jihar./Hoto: Bello Matawalle/Facebook

Karamin Minista a Ma'aikatar Tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, ya ce an tura dimbin sojojin sama da na kasa jihar Zamfara a yunkurin da ake yi na ceto daliban Jami'ar Tarayya ta Gusau da aka sace a makon jiya.

Ministan ya bayyana haka ne ranar Litinin a sanarwar da kakakin ma'aikatar Tsaro Mr Hope Attari ya fitar wadda kuma ya wallafa a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter.

A makon jiya ne wasu 'yan bindiga suka kai hari a dakunan kwanan daliban -- galibinsu mata -- a unguwar Sabon-Gida da ke Gusau da kuma cikin Jami'ar inda suka sace gommai. Sai dai shugaban Jami'ar ya shaida wa TRT Afrika cewa an ceto wasu daga cikinsu.

Wannan lamari ya tayar da hankulan 'yan Nijeriya wadanda suke ta kiraye-kiraye a ceto daliban. Shi kansa shugaban kasar Bola Tinubu ya bayar da umarni ga jami'an tsaro su kubutar da su.

Labari mai alaka: Zan bai wa masu cewa ba zan iya Ministan Tsaro ba kunya: Matawalle

Matawalle ya yi tir da sace daliban sannan ya mika jajensa ga iyayensu da jami'ar da kuma "daukacin al'ummar Zamfara bisa wannan mummuna lamari".

"A halin da ake ciki, ana tura sojojin sama da na kasa masu dimbin yawa zuwa jihar Zamfara. Za a dauki dukkan matakin da ya dace domin kare rayuka da kayayyakin 'yan Nijeriya. Ba zan iya yin karin haske a kan hakan ba saboda tsaron lafiyar sojojinmu," in ji Matawalle.

“Na damu da halin da kuke ciki kuma ina yin Allah wadai da wannan abin takaici da wadanda ake zargi 'yan bindiga ne suka aiwatar.

“Don haka ina kira ga jami'an tsaron kasar nan masu azama su matsa kaimi kana su yi amfani da duk abin da ya kamata domin kubutar da dukkan daliban da aka sace.

“Dole ne mu hada karfi da karfe don ceto daliban da aka sace,” in ji shi.

Ya kara da cewa daya daga cikin manyan muradun Shugaba Bola Ahmed Tinibu guda takwas shi ne karfafa tsaron kasa domin wanzar da zaman lafiya da walwala, yana mai cewa ma'aikatarsa za ta tabbatar da ceto daliban.

TRT Afrika