An tsinci gawar wani dan jam'iyyar adawa a Zimbabwe, bayan garkuwa da shi da aka yi a ranar Asabar a wani gangamin siyasa a wajen birnin Harare, a cewar sanarwar da jam'iyyar CCC ta fitar a ranar Litinin.
Wannan shi ne karo na biyu cikin makonni biyu da aka yi garkuwa da 'yan siyasa.
Rahotanni sun ce wasu mutane da ba a san ko su waye ba ne suka yi awon gaba da Tapfumaneyi Masaya a cikin mota, yayin da yake yakin neman zaben dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta CCC gabanin zaben fid da da gwani a kasar na ranar 9 ga watan Disamba.
Mai magana da yawun jam'iyyar Promise Mkwananzi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Talata cewa sai da aka azabtar da Masaya tare da jefar da shi a wajen birnin Harare.
An tsinci gawar Masaya sannan aka wuce da shi zuwa dakin ajiye gawawwaki da ke asibitin Parirenyatwa, mai nisan kilomita biyar daga tsakiyar birnin Harare, inda 'yan jam'iyyar CCC da ke nemansa suka gano shi, in ji Mkwananzi.
Zargin yin garkuwa da kisa
Zimbabwe tana da daɗaɗɗen tarihi na garkuwa da kuma kisan 'yan fafatukar siyasa tun daga shekarun 1980 zuwa yanzu.
'Yan adawa na yawan zargin jam'iyyar ZANU-PF mai riƙe da mulki da azabtarwa tare da kashe masu fafutuka.
An yi garkuwa da kuma kashe Masaya makonni biyu bayan dauke wani dan majalisar dokoki na jam'iyyar CCC mai suna Takudzwa Ngadziore, inda aka azabtar da kuma jefar da shi a wani wuri mai nisan kilomita 50 daga arewacin birnin Harare, sai dai ya tsira da ransa daga harin.
‘Yan sanda sun bayyana cewa an kaddamar da bincike a ranar Litinin bayan sake samun wata gawar a wurin da CCC ta ce an gano gawar Masaya, sai dai har yanzu ba a kai ga gane asa'ilin wanda kawarsa ba.
Mai magana da yawun 'yan sanda Paul Nyathi ya shaida wa Reuters a ranar Talata cewa babu wasu karin bayani da aka samu ya zuwa lokacin.
"Muna kira ga 'yan sanda da su yi aikinsu tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda aka samu da hannu a laifin garkuwar cikin gaggawa da kuma a hukunta su," in ji Mkwananzi.
Jam'iyyun adawar Zimbabwe sun yi kira da a sake gudanar da sabon zabe tun bayan da Shugaba Emmerson Mnangagwa ya yi nasarar samun wa'adi na biyu a watan Agusta.
Shugaban CCC Nelson Chamisa ya bayyana zaben a matsayin "wanda aka tafka magudi'', yayin da a nata bangaren jam'iyyar ZANU-PF mai mulki ta musanta ikirarin magudin.