IENC za ta gudanar da zabukan ne a kananan hukumomi 80 da ke wadannan jihohi domin cike gurbin ‘yan takarar da suka rasu ko kuma kotuna suka sauke su daga kan mukamansu. / Photo: AP

Rundunonin ‘yan sanda a wasu jihohi na Nijeriya sun sanar da cewa za a takaita zirga-zirga a yayin da za a yi zabukan cike gurbi a jihohi 26 na kasar a yau Asabar.

Hukumar zaben Nijeriya, INEC, za ta gudanar da zabukan raba-gardama da kuma na cike gurbi na kujerun majalisun tarayya da na jihohi a sassa daban-daban na jihohin.

Za a gudanar da zabukan ne a kananan hukumomi 80 da ke wadannan jihohi domin cike gurbin ‘yan takarar da suka rasu ko kuma kotuna suka sauke su daga kan mukamansu.

INEC za ta yi zabukan ne a jihohin Adamawa, Anambra, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Binuwai, Borno, Delta, Ebonyi, Enugu, Filato da Jigawa.

Sauran jihohin su ne Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kuros Ribas, Nasarawa, Neja, Legas, Ondo, Oyo, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.

A taron da ya gudanar na manema labarai kafin zaben, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa za a yi zabukan cike gurbi a jihohi tara domin zaben ‘yan majalisar dattawa biyu da na wakilai hudu da ‘yan majalisun jihohi.

Cikin ‘yan majalisar tarayyar da za a yi zaben cike gurbinsu har da Sanata Ibrahim Geidam wanda shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nada a matsayin minista da kuma Femi Gbajabiamila, wanda ya zama shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa.

‘Zirga-zirgar ababen hawa’

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce za ta takaita “zirga-zirgar ababen hawa a kananan hukumomi guda 6 da za a gudanar da karashen zabe na ‘yan Majalisun Jiha guda uku.”

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Juma’a da maraice ta ce za a takaita zirga-zargar a “Tsanyawa, Kunchi, Kura, Garun Mallam, Tofa da Rimin Gado.”

Shi ma kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, Mansur Hassan, ya ce za su takaita zirga-zirga a wasu yankuna na kananan hukumomin Chikun, Igabi, Kachia, Kaduna ta Kudu, Kagarko, Kudan, da Kauru.

Sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan Legas Benjamin Hundeyin ya ce za a takaita zirga-zirgar ce kawai a yankin Surelere.

Da ma dai babban sifeton ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ranar Alhamis ya ce za a takaita zirga-zirga a wasu sassa na jihohi 26 daga 12 na dare zuwa shida na maraice domin tabbatar da tsaro a lokutan zabukan.

TRT Afrika