#MEC82 : General election / Photo: AFP

An soma fitar da sakamakon zaɓe na wasu wurare da aka gudanar a Afirka ta Kudu da safiyar ranar Alhamis inda jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar ke kan gaba da kashi 41.77 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen jam'iyyar za ta rasa rinjayenta a majalisar dokokin ƙasar.

Kashi 8.9 cikin 100 na sakamakon da aka samu daga rumfunan zaɓe sun yi nuni da cewa jam'iyyar Democratic Alliance (DA) tana da kaso 27.52 yayin da jam'iyyar Marxist Economic Freedom Fighters (EFF) take da kaso 7.72, a cewar bayanai da hukumar zaɓe mai zaman kanta a ƙasar ta fitar.

A ranar Lahadi ne ake sa ran samun sakamakon ƙarshe, a cewar hukumar wadda alhakin zaɓen ya rataya a wuyanta.

Idan har sakamakon ƙarshen ya yi daidai da na farkon da aka samu, hakan zai kawo wani sauyi a yanayin siyasar Afirka ta Kudu bayan shafe tsawon shekaru 30 da gwamnatin ANC ta kwashe a kan mulki, lamarin da ka iya tilasta wa jam'iyyar ƙulla ƙawance da ɗaya ko fiye da wasu jam'iyyu don tafiyar da mulkin ƙasar.

Jam'iyyar ANC dai ta lashe zaɓukan ƙasa da ake gudanarwa duk bayan shekara biyar tun bayan babban zaɓen ƙasar na farko a shekarar 1994, wanda ya kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata.

Rinjayen Jam'iyyar ANC na cikin tsaƙa-mai-wuya

Kawo yanzu dai farin jini da goyon bayan da jam'iyyar ANC take samu sun ragu saboda rashin gamsuwa da yadda take tafiyar da mulkinta, musamman la'akari da matsaloli kamar rashin ayyukan yi da laifuffuka da ake aikawa a ƙasar da yawan rashin wutar lantarki da kuma cin hanci da rashawa.

Masu kaɗa kuri'a za su zaɓe 'yan majalisu a kowanne yanki guda tara da ake da su, sannan sabbin 'yan majalisun su kuma su zaɓi shugaban ƙasa na gaba.

Yayin da jam'iyyar ANC ke ci gaba da samun kaso mai tsoka na ƙuri'un da aka kaɗa, akwai yiwuwar shugabanta Cyril Ramaphosa ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki - sai dai idan ya ci karo da tsakon shugabanci daga cikin jam'iyyar.

Reuters