An rantsar da John Dramani Mahama a matsayin Shugaban Kasar Ghana a ranar Talata inda zai tunkari kalubalen da aka san kasar na fama da su, ciki har da cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da hauhawar farashi da rashin walwalar jama'a.
Madugun 'yan adawar mai shekaru 66, ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 7 ga Disamba da babban rinjaye inda ya sake dawowa shugabancin kasar ta Yammacin Afirka, ta biyu mafi girma wajen samar da cocoa a duniya.
Mahama ya maye gurbin Nana Akufo-Addo, wanda ya sauka bayan kammala wa'adi biyu na shugabanci, bisa dorewar dimokuradiyyar Ghana a yankin da a baya ya sha fama da juyin mulkin soja da hare-haren ta'addanci.
A yayin rantsar da shi a Accra, Mahama ya yi alkawarin "sauya fasalin'" Ghana tare da habaka tattalin arzikin kasar.
Ya kuma gode wa 'yan kasar ta Ghana saboda zabar sa da suka yi a zaben na watan Disamba.
"Akwai fata mai kyau. Yau rana ce ta farkon sabuwar dama, dama da muke da ita ta kawo suyi a shugabanci da kula da tattalin arziki.
"Dole ne mu sake sauya fasalin kasarmu Ghana da muke kauna," Mahama ya yi alkawari.
Bayan annobar COVID-19, rikicin tsadar rayuwa, kokarin kubuta daga basussukan IMF da na wasu kasashen, sun durkusa da tattalin arzikin Ghana wanda a yanzu ke farfadowa.
Alkawarurruka lokacin yakin neman zabe
Amma Mahama zai fuskanci matsin lamba na ganin cikin sauri ya cika alkawarurrukan da ya yi a lokacin zabe don magance rashin ayyukan yi da ya yi wa matasa katutu – yaki da cin hanci da rashawa – da batutuwan da ke janyo kin amince wa da salon siyasar Ghana.
“Matsakaicin dan kasar Ghana na girma tare da kosa wa da dimokuradiyyarmu,” Godfred Bokpin, Farfesa kan sha’anin kudade a Jami’ar Ghana ya fada wa Rueters.
“Mutane sun sauke nauyinsu na zabar shugaba amma suna tambayar: me suka ribata daga wannan dimokuradiyyar?”
Masu nazari da magoya bayan Jam’iyyar NDC ta Mahama na kallon kwarewarsa a siyasa da samun rinjaye da kashi biyu cikin uku a majalisar dokoki a matsayin ginshikan da za su ba su damar daukar tsauraran matakai da aiwatar da ingantattun manufofi don inganta rayuwar jama’a da jan hankulan masu zuba jari.
Rikicin makmashi
Amma matsalar makamashi da ake fuskanta za ta kawo kalubale da wuri, wanda da ma an saba da shi.
Mahama ya zama shugaban kasa a 2012, a lokacin da John Evans Attah-Mills ya mutu a kan mulki. Ya lashe zaben shugaban kasa watanni kadan baya, wanda shi ne wa’adin mulkinsa na farko, wanda ya sha fama da matsalar karancin lantarki, tabarbarewar tattalin arziki da zargin cin hanci da rashawa a tsakanin jami;an gwamnati.
A watan da ya gabata ya bayyana cewa sashen lantarki a kasar na fama da rikici, inda kiyasin farko ya bayyana cewa kudaden da ma’aikata ke bin bashi ya kai dala biliyan 2.5. Wannan mummunan yanayi na barazana ga lantarkin da ake samarwa da dakile farfado da tattalin arziki.
“Gwamnati mai barin gado ta kyale tsarin na tafiya kan magance matsalolin da ake iya gani a bayyane,” in ji Bright Simons, jami'in wata kungiya mai suna IMANI da ke Accra. “Sun bar masa manyan ciwukan”.
Simons ya ce dole ne Mahama ya yi gaggawar samar da yarjejeniyoyi da masu zuba jari a bangaren samar da makamashi, wadanda suke samar da kusan kashi 40 na lantarkin Ghana a yayin da kuma suke ci gaba da neman mafita.
Yaki da Rashawa
Kazalika, baya ga alkawarurrukan zuba jari sosai a fannin noma da kayan more rayuwa, Mahama ya kuma yi alkawarin bayar da fifiko ga yaki da cin hanci da rashawa.
Bokpin da Simons sun ce kawar da rashawa zai taimaka wajen dawo da martabar jami'an gwamnati a idanuwan 'yan kasa, amma hauhawar farashi da darajar kudin kasar na bukatar matakin gaggawa nan da nan.
A watan Nuwamba a karo na uku farashi ya hau da kashi 23.0, inda farashin kayan abinci ya ninninka.
"Za mu iya magana kan dogayen gine-gine da abubuwa masu kyau, amma gaskiya dai ita ce cewa talakan kasar Ghana na fama da jin yunwa. Dole ka bayar da fifiko ga samar da abinci," in ji Bokpin.