Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta yayin da mutane ke Sallar Asuba ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Gadan da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar ta Kano, da misalin karfe 5:20 lokacin da ake sallah, a cewar sanarwa 'yan sanda.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da TRT Afrika Hausa faruwar lamarin da kama mutumin da ake zargi, sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
Abdullahi Kiyawa ya ce bincike ya nuna cewa mutumin da ake zargi da cinna wutar Shafi'u Abubakar mai kimanin shekaru 38 ya jefa wata roba ne ɗauke da fetur cikin masallacin, sannan ya cinna wuta.
Kakakin 'yan sandan ya ce mutum 24 ne suka ƙone a masallacin, da suka haɗar da manya 20, yara huɗu.
An garzaya da duka waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawa, amma babu wanda ya mutu a hadarin, a cewar sanarwar 'yan sandan.