An kashe mataimakiyar magajin birni yankin Arewacin Kamaru da ke fama da rikicin 'yan a-ware bayan wasu mahara dauke da makamai sun yi garkuwa da ita, a cewar gidan rediyon ƙasar (CRTV) ranar Litinin.
An tsinci gawar 'yar siyasar mai suna Frida Joko cikin jini kwanaki biyu bayan an yi garkuwa da ita daga gidanta a ranar Asabar, a cewar CRTV.
Wata ƙungiyar kare hakkin bil'adama a yankin ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa 'ya'yanta sun shaida lokacin da aka yi garkuwa da ita.
A ranar Juma'a da ta gabata ma an yi garkuwa da wata ‘yar jarida mai suna Atia Tilarious Azonhw da ke amfanin da harshen Turancin Ingilishi a garin na Bamenda, kuma tun daga lokacin ba a ƙara jin labarinta ba.
'Haɗa kai ' da gwamnatin tsakiya
Babban birnin yankin Arewa maso yamma da ke amfani da harshen Turancin Ingilishi, Bamenda ya yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane da kashe-kashe tun bayan ɓarkewar rikicin 'yan a-ware a shekarar 2016.
'Yan a-waren sun sha aikata kisa tare da garkuwa da ma'aikatan gwamnati, ciki har da malamai, ko kuma zaɓaɓɓun jami'an gwamnati, waɗanda suka zarga da "haɗa kai" da gwamnatin tsakiya ta Kamaru wadda galibin masu magana da harshen Faransanci ke jagoranta.
Rikicin dai ya ɓarke ne a ƙarshen shekarar 2016 bayan shugaba Paul Biya, wanda ya shafe kusan shekaru 42 yana kan mulki a Kamaru, ya kawo ƙarshen zanga-zangar da ake yi a yankunan ƙasar biyu masu magana da Turancin Ingilishi.
Mutane da dama a yankin Kamaru masu magana da harshen Ingilishi na ganin gwamnatin tsakiya ta mayar da su saniyar-ware.
Aƙalla fararen-hula 6,000 ne dakarun gwamnati da mayaƙan 'yan a-ware suka kashe tun farkon rikicin, a cewar ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch.