An gargadi mata masu juna biyu da su yi taka-tsan-tsan wajen cin naman halittun cikin ruwa, musamman kifi da ƙaguwa da jatanlande wato shrimp da dai sauransu.
Gargadin ya biyo bayan wani bincike da Jami'ar Kiwon Lafiya ta Ghana ta gudanar, inda aka gano yadda yaduwar sinadarin Mercury da sauran ƙarafa masu nauyi a kan halittun ruwa ke haifar da mummunar illa ga yanayin girman jariran da ba a haifa ba da kuma waɗanda ake shayar da su.
Binciken ya bayyana cewa, a halin da ake ciki kusan dukkan 'yan Ghana suna mu'amala da sinadarin mercury, wanda ke shiga cikin ruwa ya kuma ratsa cikin halittun ruwan da yawancin al'ummar kasar suke ci.
“Babu wani tsari ko bincike da aka fitar wanda ya shafi kifaye da sinadarin mercury, amma akwai shaidar da ta bayyana cewa idan ƙananan kifaye suka ci sinadarin methylmercury, su kuma manyan kifaye sai su cinye su, hakan kuma sai ya tara musu sinadarin mai yawa a jikinsu, " a cewar Shugaban Jami'ar Farfesa Richmond Aryeetey.
Shugaban ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ghana (GNA) cewa yawan sinadarin mercury da ake fitarwa a cikin al'umma ta kasar da kuma cikin ruwan rafi ba tare da la'akari da illarsa ba balle a yi kokari dakile yaduwarsa.
A karshe yakan haifar da mummunar illa ga lafiyar jarirai da kuma wadanda ba a haifa sakamakon mu'amalar da iyayensu mata suka yi da shi.
Farfesan ya ƙara da cewa, ba za a iya kawar da ɓarnar da ake samu sakamakon shigar wasu manyan ƙarafa a jikin jarirai ba a lokacin da ake dauke da cikinsu da kuma yayin da ake shayar da su.
“Mercury karfe ne, idan aka ƙona shi ya shiga iska da ruwa, sai ya koma wani abu mai guba da ake kira methyl mercury, wanda kifi da sauran halittun cikin ruwa ke cinyewa, sai dai ƙananan kifaye ba sa iya cin adadin da manyan kifaye ke iya ci.
"Amma daga baya manyan ke cinye ƙananan kifin wanda ke ƙara musu adadin gubar a jikinsu,”a cewar Farfesa Aryeetey.
Farfesa Aryectey ya ce a duk shekara, ana fitar da kimanin tan 81 na Mercury a cikin muhalli musamman ta hanyar ƙona ire-iren ƙarafa a lokaci guda.
Mu'amala da sinadarin mercury, komai ƙanƙantarsa, na haifar da mummunar illa ga lafiyar jikin ɗan'adam sannan yana zama barazana ga ci gaban ɗa a cikin mahaifa da kuma bayan an haife shi.
Fitar da yawan sinadarin mercury na iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki, musamman ga jarirai da ƙananan yara da mata masu juna biyu.
Yana iya lalata tsarin girman jiki da lalata haɓakar ƙwaƙwalwa ta jarirai da yara da aikin jijiya da huhu da ƙoda da kuma fatar jikin ɗan'adam sannan yana haifar da matsala ga sassan gani da ji.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana sinadarin Mercury a matsayin daya daga cikin manyan sinadarai goma masu guba ko kuma nau'in sanadarai masu illa ga lafiyar jama'a.
Don rage wannan hadarin ga lafiyar jarirai, binciken Jami'ar Kiwon Lafiyar Ghanan ya shawarci mata masu juna biyu da suna cin kananan kifaye a cikin nau'in abincinsu masu gina jiki.