Hukumomi sun sha yin alƙawarin kakkaɓe matsalar hare-haren ƴan bindiga musamman a arewa maso yammacin Nijeriya amma har yanzu lamarin ya ci tura./Hoto:OTHER

Wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Kajuru da ke Kaduna a arewacin Nijeriya ranar Lahadi inda suka ƙona aƙalla mutum 12 da ransu, a cewar mazauna yankin.

Harin, wanda ƴan bindigar suka kai a ƙauyen Gindin Dutse Makyali, ya yi sanadin jikkatar mutum 15 bayan an cinna wa gidajensu wuta, in ji Isa Yusuf, wani shugaban matasan yankin a hira ta wayar tarho da kamfani dillancin labarai na Anadolu.

"Sun yi ta buɗe wuta, abin da ya sa muka ji tsoron fita daga gidajenmu. Don haka, sai suka cinna wuta a gidajen mutane inda suka kashe mutum 12 a cikin gidajensu, kana mutum kusan 15 suka ji munanan raunuka," a cewarsa.

Isa Yusuf ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun ƙone gidaje 17, yana mai cewa an kai mutum 15 da suka ji raunuka asibitin da ke kusa domin kula da su.

Mai magana da yawun ƴan sandan Kaduna Mansur Hassan ya tabbatar wa Anadolu aukuwar lamarin, yana mai cewa an tura ƙarin ƴan sanda na musamman yankin domin "hana kai ƙarin hare-hare da kuma kwantar da hankulan mazauna yankin."

'Kashe ɗan sanda'

A jihar Zamfara, hukumomi sun tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari wasu wurare a ƙaramar hukumar Zurmi ciki har da ofishin ƴan sanda ranar Lahadi.

Ganau sun ce ƴan bindigar sun kai hari a garin ne da maraice inda suka kashe mutum bakwai har da wani ɗan sanda.

Sun ƙara da cewa ƴan bindigar sun je garin ne domin yin ramuwa bisa kisan wasu abokansu biyu da ƴan banga suka yi.

Kafofin watsa labaran Nijeriya sun ambato kakakin rundunar ƴan sandan Zamfara Yazid Abubakar yana tabbatar da kai harin, ko da yake bai yi ƙarin bayani ba.

TRT Afrika da abokan hulda