Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya ya sha alwashin magance rashin tsaro a kasar mai mutum fiye da miliyan 200./Hoto:Rundunar yan sandan Nijeriya

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce za ta tura manyan jami'anta fadin kasar domin inganta fannin leken asirinta da nufin magance matsalar rashin tsaro.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Talata da maraice.

Sanarwar ta ambato Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya Olukayode Adeolu Egbetokun yana bayar da umarnin tura 'yan sanda 54 masu mukaman Mataimakan Kwamishinonin 'yan sanda "domin su jagoranci sassan leken asiri na yankuna da jihohi da ke fadin kasar."

Ya dauki matakin ne bisa "burinsa" na "karfafa sassan leken asiri na rundunar a kowane mataki da ke fadin kasar a matsayin wata hanya ta shawo kan matsalar aikata laifuka," in ji sanarwar.

Hakan na faruwa ne a yayin da kasar ke ci gaba da fama da matsalolin tsaro musamman garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna, har ma da Abuja.

Ko a makon jiya mutane sun gudanar da zanga-zanga a Abuja domin matsa lamba kan gwamnati da jami'an tsaro su dauki matakin gaggawa kan sace-sacen jama'a da ke addabar babban birnin kasar.

Wani sabon rahoto da kamfanin tsaro mai zaman kansa na Beacon Consulting a Nijeriya ya fitar ya ce mutum 9, 734 sun rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci a fadin kasar a shekarar 2023.

Ya ce an sace mutum fiye da 5,000 a kasar a shekarar 2023.

TRT Afrika