Kungiyar M23 da ke samun goyon bayan wasu sojojin Rwanda kimanin 4,000 a cewar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka tana rike da yankuna da dama na gabashin DRC, yankin da ke fama da rikici. / Hoto: AFP

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da Shugaban kasar Kenya William Ruto sun bukaci da a gaggauta tsagaita bude wuta a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (DRC) yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar.

"Sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya tattauna da shugaban kasar Kenya William Ruto domin tattauna rikicin da ake fama da shi a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, da suka hada da kwace Goma da Bukavu da kungiyar M23 da ke samun goyon bayan Rwanda suka yi ba tare da amincewa ba," a cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar a ranar Juma'a.

Shugabannin biyu sun sake jaddada aniyarsu ta ganin an cimma matsaya ta diflomasiyya kan rikicin.

Kwana guda kafin haka, Amurka ta ce za ta kakaba takunkumi kan wani ministan gwamnatin Rwanda da wani babban jami'in kungiyar masu dauke da makamai bisa zarginsu da hannu a rikicin.

An buƙaci Rwanda ta janye sojojinta

A cikin wata sanarwa ta diflomasiyya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani a farkon wannan watan, Amurka ta ce idan ana so a samu kwanciyar hankali a yankin akwai buƙatar sojojin Rwanda "su janye sojojinsu da manyan makamai" daga DRC.

Har ila yau, a ranar Juma'a, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda a karon farko, kan goyon bayan da take bai wa 'yan tawayen M23 a kan makwabciyarta DRC, tare da yin kira ga Kigali da ta gaggauta janye sojojinta.

Kudurin wanda "ya yi kakkausan Allah-wadai da hare-haren da 'yan tawayen M23 ke ci gaba da kaiwa Arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron Rwanda," an amince da shi gaba daya.

Har ila yau, "tana kira ga dakarun tsaron Rwanda da su dakatar da goyon bayan M23 da kuma janyewa daga yankin DRC ba tare da wani sharadi ba."

'Babu kusan wani sojan Kongo da ke yaƙi'

Hakan ya zo ne bayan da mayakan na M23 suka ci gaba da samun nasara a fagagen daga daban-daban a ranar Juma’a.

Kungiyar M23 da ke samun goyon bayan wasu sojojin Rwanda kimanin 4,000 a cewar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka tana rike da yankuna da dama na gabashin DRC, yankin da ke fama da rikici.

Yunkurin ci gabanta ya sa dubban mutane tserewa.

Mayakan sun kwace iko da babban birnin lardin Kivu ta Kudu Bukavu a ranar Lahadin da ta gabata, makonni bayan da suka kwace Goma, babban birnin Kivu ta Arewa kuma babban birnin da ke gabashin kasar.

A baya dai kwamitin sulhun ya yi kira da a gaggauta tsagaita buɗe wuta ba tare da wani sharadi ba, amma a ranar Juma'a dukkan kasashen da suka hada da mambobin Afirka uku sun nuna yatsa a Kigali.

TRT World