Ambaliyar ruwan da aka yi a Libya, wacce ta kashe dubban mutane a birnin Derna, ta raba fiye da mutum 43,000 da muhallansu, a cewar Hukumar Kula da Masu Kaura ta Duniya ranar Alhamis.
Wata mahaukaciyar guguwa mai kama da tsunami wadda ake kira 'Daniel' ta sa madatsan ruwa biyu sun karye lamarin da ya haddasa gagarumar asarar rayuka da batan mutane ranar 10 ga watan Satumba.
Ambaliyar ta ragargaza illaharin unguwanni tare da tafiya da mutane cikin teku suka bace.
Alkaluman yawan mutanen da suka mutum ya haura 3,300 -- amma lamarin na iya fin haka inda kungiyoyin kasa da kasa ke ƙiyasta cewa yawan mutanen da suka mutu zai kai 10,000.
"An ƙiyasta cewa mutum 43,059 ambaliyar ruwan ta raba da muhallansu a arewa maso gabashin Libiya," in ji Hukumar Ƙaura Ta Duniya IOM, ina ta ƙara da cewa "a yanzu rashin ruwa ya sa mutane da dama a Derna suna barin yankin zuwa wasu yankunan."
"Ana tsananin buƙatar abinci da ruwan sha da likitocin da za su ba da taimako kan lafiyar ƙwaƙwalwa," ya ce.
Sai dai intanet da layukan waya sun dawo aiki bayan datse su da aka yi tsawon kwana biyu, sakamakon zanga-zangar da da aka yi a ranar Litinin, wacce ta sa mazauna yankunan da ke cike da fushi suka zargi hukumomi kan yawan mutuwar mutanen.
Hukumomi sun alakanta katsewar sadarwar kan wata abin da ya faru a Derna, amma wasu masu amfani da intanet da kuma masu sharhi sun ce da gangan aka katse sadarwar.
Firaministan kasar da ke zaune a birnin Tripoli Abdulhamid Dbeibah ya sanar da cewa an dawo da hanyoyin sadarwar a gabashi, a wani saƙo da aka wallafa a shafin X a ranar Alhamis.
An samu rarrabuwar kai inda gwamnatoci biyu ke mulki sakamakon yakin da ake yi a Libiya, da ta Dbeibah da MDD ke goyon baya da kuma bangaren da Khalifa Haftar ke goyon baya.
- An gano wadanda ake zargi -
Tun shekarun 1990 ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yawan yi ya jawo madatsun ruwan sun tumbatsa inda har suka fara tsagewa, a cewar babban mai shigar da ƙara na Libiya, lamarin da ya sa mazauna yankin suka zargi humomi da rashin mayar da hankali.
Mafi yawan ababen more rayuwa na Libiya sun lalace tun bayan rikicin da ya balle a kasar wanda NATO ta ba da goyon baya har aka yi tashin hankalin da ya jawo hambarar da Shugaba Moamer Ghaddafi.
Dakarun Haftar sun ƙwace iko da Derna a 2018, wani yanki da a baya ke ƙarƙashin ikon masu tsattsauran ra'ayin addini, sannan yanki ne da ya yi ƙaurin suna wajen yin bore tun lokacin mulkin Ghaddafi.
Masu zanga-zanga sun taru a gaban babban masallacin birnin Derna ranar Litinin suna ihun nuna adawa da majalisar dokokin gabashin Libiya da shugabanta Aguilah Saleh.
A wata hira da aka yi da atoni janar na Libiya a talabijin Al-Seddik al-Sour ya sha alwashin "samar da sakamako da gaggawa" kan binciken abin da ya jawo bala'in.
Ya ƙara da cewa tuni aka gano wadanda ake zarginsu da cin hanci ko rashin mayar da hankali kan lamari, amma bai fadi sunayensu ba.
Sai dai duk da haka mazauna Derna na fuskantar sabbin barazana.
A wannan makon MDD ta yi gargadi kan yiwuwar barkewar cututtuka ka iya jawo wani mummunan yanayi a yankunan da lamarin ya shafa.
Jami'an yankin da hukumomin ba da agaji da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya sun damu a kan barazanar barkewar cututtukan, musamman daga shan ruwan da ya gurbata da kuma rashin tsaftar muhalli, in ji MDD.
Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Libiya ta yi gargadin cewa ainihin hanyoyin ruwan sha a yankun sun gurbata tare da umartar mazauna da kat su yi amfani da shi.