Ambaliyar ruwan ta fi yin barna a yankin Derna, a cewar hukumomi/ Hoto: / Photo: AFP / Photo: Reuters

Hukumomi a Libya sun bayyana cewa mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa a kasar sun zarta 6,000.

Sabbin alkaluman da gwamnatin hadin-kai ta kasar Libya ta fitar ranar Laraba sun kara da cewa dubban mutane ne suka bata sakamakon wannan bala'i.

A yayin da yake hira da kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya, Saadeddin Abdul Wakil, karamin sakataren Ma'aikatar Lafiya na gwamnatin kasar, ya ce wadanda suka mutu sun wuce 6,000, kuma dubbai sun bata.

"Alkaluman wadanda suka mutu na wucin-gadi ne, kuma sun shafi dukkan wuraren da ambaliyar ruwan ta yi wa barna, sannan lamarin ya fi shafar birnin Derna," in ji shi, yana mai nuna damuwa cewa adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa nan da awanni kadan masu zuwa.

Labari mai alaka: Mummunar ambaliyar ruwa ta kashe fiye da mutum 5000 a birnin Derna na Libya

Wakil ya kara da cewa asibitocin gwamnati da ke yankin da lamarin ya shafa sun daina aiki, yana mai cewa suna kokari don ganin sun gyara asibitoci 10 da cibiyoyin bayar da magani 20.

Kungiyoyin bayar da agaji na Red Cross da Red Crescent a ranar Litinin sun ce mutanen da suka bata bayan ambaliyar ruwan sun zarta 10,000.

Mummunar ambaliyar ruwa mai tafe da mahaukaciyar guguwa ta fada wa yankunan gabashin Libya, musamman Benghazi, Al Bayda da Al-Marj, da kuma Soussa da Derna.

Hukumar Kula da Kaura ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 360,000 ne suka rasa matsugunansu a kasar.

“Akalla mutum 30,000 ne suka rasa matsugunansu a Derna sakamakon mahaukaciyar Guguwa mai suna Daniel, yayin da mutum 3,000 suka rasa nasu gidajen a Albayda, 1,000 a Almkheley, da kuma 2,085 a Benghazi,” in ji hukumar a sakon da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba.

AA