Ambaliyar ruwan ta rusa gine-gine da kuma lalata dukiyoyi. Hoto/Reuters

Kusan mutum 10,000 ake fargabar sun bace sakamakon wannan ambaliya, kamar yadda kungiyar agaji ta International Federation of the Red Cross and Red Crescent Societies ta sanar a ranar Litinin.

Hukumomi a gabashin Libiya sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa ya kai 3,000.

“Majiyoyinmu masu zaman kansu sun tabbatar mana da cewa adadin wadanda suka rasu ya kai dubu goma zuwa yanzu,” kamar yadda Tamer Ramadan ya bayyana, shugaban IFRC a Libiya ya shaida wa manema labarai daga Tunisia.

Ministan Lafiya a kasar ya bayyana cewa akwai dubban mutane da har yanxu ba a gansu ba.

Gwamnatin Libiya ta ce tuni ta binne mutum 700 daga cikin wadanda suka rasu.

Biranen da wannan ambaliyar ta fi shafa sun hada da Derna da Benghazi da Bayda da Al Marj da kuma Soussa.

A birnin Derna kadai, akalla mutum 2,300 suka rasu sakamakon ambaliyar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.

Kusan iyalai 7,000 suke gararamba a wuraren da lamarin ya faru, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar inda suka kara da cewa ana ci gaba aikin ceto.

Abdul Hamid Dbeibeh, wanda shi ne shugaban gwamnatin hadin kai ta Libiya da ke Tripoli ya sanar da zaman makoki na kwana uku a duka wuraren da wannan bala'i ya fadamawa.

Reuters