Tebboune ya tuna da irin zaluncin da sojojin mulkin mallaka na Faransa suka aikata. / Hoto: Reuters

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya ƙaddamar da wata sabuwar caccaka kan Faransa dangane da tasirin da mulkin mallakar da ƙasar ta yi wa Aljeriya.

Ya caccaki Faransar ne a lokacin da ya gudanar da jawabi ga ƙasar a gaban duka majalisun ƙasar inda ya gabatar da irin nasarorin da ya samu a wa'adinsa na farko na shugabancin ƙasar tsakanin 2019 zuwa 2024 da kuma ƙara fitar da manufofinsa a wa'adinsa na biyu wanda ya fara a wata Satumba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.

Tebboune ya bayyana cewa Aljeriya na so Faransa ta amince da irin laifukan da ta aikata a lokacin mulkin mallaka tsakanin 1830 zuwa 1962, inda ta jaddada cewa ƙasar ba ta buƙatar wata diyya.

"Muna neman dawo da mutuncin kakanninmu," in ji shi

'Yan Aljeriya da aka kashe

"Adadin 'yan Aljeriya da aka kashe a tsawon shekara 132 na mulkin mallaka ya kai miliyan 5.6, kuma babu adadin kuɗin da za a biya da za su kasance diyyar ko da mutum ɗaya da aka kashe a lokacin gwagwarmayar," in ji shi.

Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin Aljeriya da Faransa, lamarin da ya kai ga janye jakadan Aljeriya tare da kiran jakadan Faransa.

Hukumomin Aljeriya sun danganta wannan tashin hankalin da "mugayen ayyuka da jami'an leken asirin Faransa na kasashen waje suka aikata a kasar Aljeriya."

Tebboune ya kuma tuno da irin ta'asar da sojojin Faransa 'yan mulkin mallaka suka aikata, musamman a karkashin Janar Thomas Robert Bugeaud, gwamnan-Janar na Aljeriya daga 1841-1847, wanda ya bayyana a matsayin "kisan kare dangi."

Ya bayyana cewa har yanzu Faransa na riƙe da kawunan ƙwarangal fiye da 500 na 'yan Aljeriya waɗanda ta fille wa kai a ƙarni na 19 inda aka kai kawunan Paris.

"Mun yi ƙoƙarin karɓo kawuna 24 kacal," kamar yadda ya bayyana.

AA