Tawagar Ghana ta Black Stars ta baje kolin tufafin al'adar kasar inda 'yan tawagar suka sanya tufafin kente. Hoto: Others

Daga Emmanuel Onyango

Tun da tawagogin kasashen Afirka suka fara isa Côte d'Ivoire domin gasar kofin Afirka da za a fara ranar Asabar aka fara baje-kolin kayayyakin kawa na al'adun kasashen Afirka.

Tawagogin kasashen Nijeriya da Ghana da Gambia da Senegal da kuma Guinea suna daga cikin tawagogin da suka isa kasar Ivory Coast domin gasar inda suke sanye da tufafin gargajiya.

'Yan wasan Guinean sun isa cikin tufafi mai kyau da ake ce wa lepi, daya daga cikin tufafi masu kima a kasarsu. Tawagar da ake ce wa National Elephants za ta yi wasanta na farko ne ranar Litinin inda za ta kara da Indomitable Lions din Kamaru.

Tawagar Brave Warriors ta Namibia. Hoto: Namibia Football Association

Tawagar Ghana ta Black Stars ta isa Abidjan cikin tufafin kente, kayan da aka fi sanin kasar da shi. Tawagar za ta kara da Cape Verde a wasanta na farko ranar Lahadi.

Tawagar Gambia ta Scorpions ta samu matsala a jirgin sama. Hoto: Others.

Super Eagles din Nijeriya Kaftan suka saka, daya daga cikin tufafin da aka fi sakawa a kasar, a lokacin da suka isa kasa mai masaukin gasar.

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta buga wasanta na farko ranar Lahadi. Hoto: Bashir Ahmad/X

Za su kara da Equatorial Guinea ranar Lahadi Sunday inda za su fara fafatukar neman cin kofin Afirka.

Tawagar kwallon kafar Guinea, National Elephants, za ta yi wasanta na farko ranar Litinin. Hoto: Fédération Guinéenne de Football/X

'Yan wasan Gambia sun mance da rashin jituwarsu da hukumar kwallon kafar kasar kan rashin kyautar samun gurbin shiga gasar AFCON inda suka isa Abidjan sanye da fararen tufafi.

Tawagar da aka fi sani da Scorpions, ta kai ga matakin kusa da dab da na karshe a gasar AFCON dinta ta farko shekara biyu da suka wuce.

Tawagar Brave Warriors ta Namibia sun saka tufafi mai launin tutar kasar, shudi da kore da ja.

Tawagar Teranga Lions ta Senegal tana cikin tawagogin da ake ganin za su iya lashe gasar cin kofin Afirka. Hoto: Others

Tawagar kasar Senegal, Lions of Teranga ita ma ta isa cikin wani salo na ban-sha'awa. Shugaba Macky Sall ya yi mata fatan nasara a gasar.

Gasar cin kofin Afirka ta AFCON ita ce gasar kwallon kafa mafi girma a Afirka kuma kasashe 24 ne za su fafata a gasar ta wannan shekarar.

TRT Afrika