"Iyalai gaba daya sun mutu" a hadarin, in ji su, yayin da suke tserewa yakin da ake ci gaba da yi inda RSF ke sake kutsawa Sennar. / Photo: Reuters

Masu fafutukar tabbatar da dimokradiyya a Sudan sun ce kimanin mutane 25 ne suka nutse a Kogin Nilu a lokacin da suke kokarin tsere wa fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai a kudu maso gabashin kasar.

"Kimanin 'yan kasar 25, yawancinsu mata da yara ne suka mutu sakamakon nutsewa a hatsarin kwale-kwale a lokacin da suke tsallaka Kogin Nilu a jihar Sennar da ke kudu maso gabashin kasar, in ji wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis.

Kwamitin dai na daya daga cikin daruruwa a Sudan da suka saba shirya zanga-zangar neman tabbatar da dimokuradiyya tare da hada kai agajin sahun gaba tun bayan da aka fara yakin da ake yi tsakanin sojoji da dakarun sa kai na RSF a bara.

"Iyalai gaba daya sun mutu" a hadarin, in ji su, yayin da suke tserewa yakin da ake ci gaba da yi inda RSF ke sake kutsawa Sennar.

Ƙananan jiragen ruwan katako

A ranar Asabar, RSF ta sanar da cewa ta ƙwace wani sansanin soji a Sinja, babban birnin jihar Sennar, inda sama da rabin miliyan suka nemi mafaka daga yakin.

Shaidu sun kuma bayar da rahoton cewa RSF din ta ratsa kauyukan da ke makwabtaka da su, tare da tura mazauna yankin tserewa cikin kananan kwale-kwale na katako a Kogin Nilu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 55,000 ne suka tsere daga kasar Sinja cikin kwanaki uku.

Hukumomin yanki jihar Gedaref da ke makwabtaka da jihar sun yi kiyasi a ranar Alhamis cewa kimanin mutane 120,000 da suka rasa matsugunansu ne suka isa a wannan mako.

TRT Afrika