An naɗa McKenzie - shugaban jam'iyyar Patriotic Alliance (PA) a matsayin Ministan Wasanni, Fasaha da Al'adu. Hoto / Patriotic Alliance

Duk da cewa Gayton McKenzie ya ga wani sauyi mai ban mamaki a rayuwarsa na zama wani babba a siyasance a Afirka ta Kudu, to ba zai taɓa mantawa da hukuncin da aka taɓa yanke masa na zama a gidan yari ba, bayan kama shi da laifin fashi a banki.

A wannan makon ne aka naɗa tsohon shugaban kungiyar ‘yan daba mai shekaru 50 a cikin majalisar ministocin kasar Afirka ta Kudu yayin da kasar ta kafa gwamnatin hadin kan kasa (GNU) da Shugaba Cyril Ramaphosa ya ƙaddamar.

Hakan dai na zuwa ne bayan da jam'iyyar ANC mai rinjaye ta rasa rinjayen 'yan majalisar dokokin ƙasar inda aka tilasta mata shiga ƙawance da jam'iyyun adawa.

An naɗa McKenzie - shugaban jam'iyyar Patriotic Alliance (PA) a matsayin Ministan Wasanni, Fasaha da Al'adu.

Kuma a ranar Laraba aka rantsar da shi tare da sauran takwarorinsa na majalisar ministocin, kuma ko a wajen sai da ya sanya mutane raha cikin barkwanci wanda ke nuni da irin laifin da ya aikata a baya.

"Lokaci na karshe da wani alkali ya buƙaci na zauna, sai zaman ya zo da yanke min hukunci na tsawon shekara 10 a gidan yari," ya faɗa cikin raha a lokacin da alkalin alkalan ƙasar Raymond Zondo ya buƙaci ya zauna don ya sanya hannu kan takardar rantsuwar zama minista.

"Wannan ya daɗe da wucewa)!" Alkalin Alkalan ya amsa da dariya tare da wadanda suka halarci taron.

Magoya bayan McKenzie sun ce labarin rayuwarsa daga zama shugaban kungiyar ‘yan daba a lokacin da yake da shekaru 16 zuwa zama minista a gwamnati, lamarin da ba a taɓa yin irinsa ba, wani ƙwarin gwiwa ne na shawo kan matsalolin rayuwa.

“Rayuwata ta ƙunshi shiga da fita gidan yari. Ba da daɗewa ba na zama wanda ake nema ruwa a jallo a sassa daban-daban na ’yan sanda. An kama ni ina da shekaru 21 a ƙarshe, ”in ji Ministan a cikin wasu jerin saƙonni da ya wallafa a shafin X.

"Na bayyana a kotu kuma an yanke min hukuncin daurin shekaru 17 a gidan yarin Grootvlei."

A lokacin, zuwa gidan yari tamkar alama ce ta girmamawa, in ji McKenzie. "Ba da daɗewa ba na yi shugabancin fursunonin gidan yarin gaba ɗaya kuma babu abin da zai faru a gidan yarin ba tare da na faɗa ba."

Bayan an sake shi ya tsunduma cikin harkokin kasuwanci daban-daban - tun daga sayar da kifi, da gudanar da gidajen rawa da kuma saka hannun jari a harkar hakar ma'adinai.

Ya kuma kafa kamfanin buga littattafai da sayar da litattafai masu motsa rai daga abubuwan da suka faru a rayuwarsa.

Ya zama miloniya ta ƙiyasinsa. Amma sai da ya yi hatsarin mota kafin ya kai ga fara ganin sauyin rayuwa.

Harkokin siyasa

Ba da jimawa ba ya mayar da hankalinsa kan harkokin siyasa inda ya kafa jam’iyyarsa ta Patriotic Alliance a shekarar 2013 wacce ke da matsananciyar matsaya a kan harkokin shige da fice.

Ta lashe kashi biyu cikin 100 na kuri'un da aka kada a kasar a zaben na ranar 29 ga watan Mayu, tare da nuna ƙwazo a lardin Western Cape, inda ta samu kashi takwas cikin 100 na kuri'un. Ta lashe kujeru tara na Majalisar Dokoki ta Kasa.

Lokacin da Shugaba Ramaphosa ya fara zawarcin jam'iyyun da za a kafa gwamnatin hadin gwiwa, McKenzie ya fito fili ya bayyana sha'awarsa ga ma'aikatar harkokin cikin gida, mai kula da shige da fice. Sai dai ya ƙara da cewa zai kasance mai gaskiya a tattaunawar.

"Ba mu da isassun kujerun da za su sanya mu a matsayin da za mu shata layi," in ji shi a cikin wani sakon X.

"Za mu saurari shawarar shugaban kasa kuma za mu mutunta 'yancin da kundin tsarin mulki ya ba shi na yanke shawarar wanda yake so a majalisarsa."

Mambobin zartarwa na Afirka ta Kudu. Gayton McKenzie yana zaune a gefen hagu daga nesa a layin gaba. Hoto / SA Presidency

Majalisar ministocin Ramaphosa mai mambobi 32 tana da ƙarin mataimakan ministoci 43 kuma ta sha suka daga jama'a da cewaan debi mutane da yawa a lokacin da ake cikin halin taɓarɓarewar tattalin arziki. Duk da haka, McKenzie yana da kyakkyawan fata game da sakamakon gwamnatin haɗin gwiwar.

"Rayuwa ta koya mani cewa wani lokacin yana da kyau a yi fada daga ciki fiye da daga waje, hakan kuma ya koya min cewa a cikin tattaunawar ba za ku taba samun duk abin da kuke so ba. Ina son Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, ban samu ba," kamar yadda ya wallafa a shafin X bayan sanar da jerin sunayen ministocin.

McKenzie ya yi alkawarin bayar da dukkanin albashinsa na majalisa ga gidauniyar Joshlin Smith da ke kula da yaran da suka ɓace, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito.

“Kashi 100 na albashina zan bai wa gidauniyar Joshlin Smith mai kula da harkokin yaran da suka ɓace na tsawon zamana a majalisar, kashi 100 na albashina ba 80% ko 50% ba... Saboda ban zo nan don kuɗi ba. Na zo ne domin in sauya rayuwar mutanenmu,” in ji shi.

TRT Afrika