"Fiye da 'yan ta'adda 100 aka kashe tun fara kai hare-haren," kamar yadda rundunar sojin ta faɗa a sanarwar ta baya-bayan nan / Hoto: AA

Rundunar sojin Nijar ta sanar da cewa ta kashe ‘yan ta’adda sama da 100 a hare-haren da ta kai ta sama da ta ƙasa, a wani mataki na mayar da martani ga wani ƙazamin harin da aka kai wa sojoji kusa da kan iyakar Burkina Faso.

Wata gamayyar ƙungiyoyin masu tada ƙayar baya sun kashe dakaru 20 da kuma farar hula ɗaya a yankin Tera da masu ikirarin jihadi suka yi wa kaka-gida ranar 25 ga watan Yunin da ya gabata, a wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a ranar Alhamis.

"Fiye da 'yan ta'adda 100 aka kashe tun fara kai hare-haren," kamar yadda rundunar sojin ta faɗa a sanarwar ta baya-bayan nan, tana mai cewa tana ci gaba da kai hare-haren.

Rundunar ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar a baya cewa ta kashe ‘yan ta’adda kusan 30 a yankin washegarin bayan harin Tera tare da lalata musu hanyar da suke bi wajen kai hare-hare a wani samame da ta kai.

Tera yana cikin yankin Tillaberi mai iyaka da Mali da Burkina Faso inda 'yan tawaye masu alaƙa da Al-Qaeda da kungiyar IS suka kwashe kusan shekaru goma suna tada ƙayar baya.

Ana yawan kai wa fararen hula hari a yankin daga masu jihadi, lamarin da ya sa mutane da dama ƙaurace wa gidajensu.

Manyan motocin dakon kaya daga Nijar su ma suna bi ta Tera, suna zuwa duk wata daga tashar ruwan Lome ta Togo, ta arewacin Burkina Faso.

Reuters