Daga Sylvia Chebet
Kamar yadda idanuwa ke gani, danyen garin cobalt ne tare da tsaftatacciyar wayar cobalt ne a cikin buhunhuna a wannan waje, kamar ka ce wani ne ya kulle su tare da manta wa da su.
Ajiyayyun hodar cobalt mai yawan tan 13,000, daidai da yawan kaso 70 na yawan hodar da aka samar a duniya a 2022 ne aka gani jibge a Tenke Fungurume da ke kusu maso-gabashin Kongo.
Congo ce kasa ta biyu a duniya da ta fa yawan fitar da albarkatun cobalt wanda ke a waje mai girman sukwaya kilomita 1,600, kamar yadda AFP suka rawaito.
Bayanan kamfanin sun bayyana cewa wajen hakar ma’adinan mallakin China na samar da tan 20,000 na copper da tan 1,500 na cobalt a kowanne wata a shekarar da ta gabata.
An fara tattara ma’adinan da yawa daga watan Yulin 2022, a lokacin da gwamnati ta hana kamfanin fitar da albarkatun, kuma a watan Afrilun bana aka janye wannan hani.
“Wata tara aka dauka ana samar da kayan kuma ana ajiye su. Karancin kudi a lalitar gwamnatin Kongo ne ya janyo hakan,” in ji wani kwararre kan hakar ma’adinan tsaunin karafa.
Tare da janye haramcin fitar da ma’adinan zuwa kasashen waje, kamfanin China Molybdenum Ltd ya fara kokarin fitar da kayan da ya tara.
Harry Fisher, mai nazari a Cibiyar Leken Asirin Hakar ma’adinai ta Benchmark ya ce za a iya daukar tsawon watanni goma ana jigilar fita da kayan da kamfanin ya tara, inda ya yi nuni da hakan na iya kawo cikas wajen kwashe kayayyakin.
Vincent Zhou, kakakin kamfanin na China ya ce manufarsu ita ce su fitar da kayan duba da bukatar da ake da ita a kasuwanni.
Duba ga farashi
Farashin cobalt ya karye da wajen kaso 65 daga watan Mayun shekarar da ta gabata – daga dala 40 awo daya zuwa dala 14, kamar yadda Fastmarkets da ke kawo rahotannin farashin ma’adanai suka sanar.
Tsoron da aka fara yi shi ne idan aka saki dukkan ma’adanin na cobalt din da ake da shi a Tekke Fungurume zuwa kasuwannin duniya a lokaci guda, kasuwar za ta yi raga-raga, da ma kasuwar ta yi kasa sosai ballantana kuma a ce an sake shi dukka a lokaci guda.
A yanzu dai kusan an ma fitar da rai kan dawowar hada-hada a Tekke kamar yadda take a baya.
“Babu abin da ya shafi farashin cobalt”, in ji Zhou Jun, mataimakin shugaban kamfanin CMOC na China da ke Tenke Fungurume.
“Za a sayar da mafi yawan cobalt din a hankali da kadan-kadan a tsawon lokaci na fitar da kayayyaki”.
A watan Afrilu ne cibiyar Benchmark ta sanar da darajar cobalt din da aka boye da ya kai na dala miliyan 340.
Sannan copper din da ake da shi kuma ya kai na dala biliyan 1.5, duba da farashin musayar karafa a Landan.
A kowacce shekara ana samar da miliyoyin tan na copper a duniya baki daya, wanda hakan ke nufin akwai yiwuwar kayan da aka tara a Tenke Fungureme ya karye sosai.
Amma kuma, idan akasake shi gaba daya, zai tsawaita lokacin da za a dauka ana sayar da shi da rahuwa sosai.
Makamashi marar illa
Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo ce ke samar da sama da kaso 70 cikin dari na cobalt da ake samu a duniya, kuma ita ta fi kowacce a Afirka fitar da copper.
Karafan biyu na da muhimmanci wajen samar da makamashi marar illa.
Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta bayyana cewa dukkan motoci masu aiki da lantarki na bukatar wani adadi mai yawa na cobalt don amfani a cikin batira, daura wayoyi da kuma yin caji.
IEA sun yi hasashen cewa bukatar da ake da ita ta motoci masu lantarki za ta karu a shekaru masu zuwa, wanda hakan zai sanya karuwar bukatar copper da ake da ita.
Baya ga batiran motoci masu aiki da lantarki, ana amfani da cobalt a batiran da ake sakawa wayoyin hannu, tablet da na’ura mai kwakwalwa.
Amma kuma a yayin da yake labara mai dadi ga sauran duniya, amma a gida abun ba shi da dadi sam.
“Kamar yadda kuka sani, ana samun ribar ne a wajen kasar. Inda kasar da jama’ar kasar suke asara kenan. Dukkan albarkatun kasar na barin kasarmu cikin taluci.
Har yanzu ba mu da hanyoyi masu kyau, makarantu ko asibitoci,” inji Papy Masudi Radjabo, wani mai fafutukar ma’adanai da ke da kungiyar gwagwarmaya ta Filimbi yayin tattaunawarsa da TRT Afirka.
Yankin Kongo da ke samar da ma’adanan kasa na da babbar hanya da ke danganawa ga tashoshin jiragen ruwa na Tekun Indiya kamr su Durban ko Darussalam.
Amma hanyoyin na cike da matsaloli, marayi na kai hari, ana samun cunkoson ababan hawa.
A yanzu, Kongo za ta yi farin ciki idan aka kawo karshen abubuwan da ke faruwa a Tenke Funfurume.