Dada Kudra Maliro
Pierre Sedi ya zama kyakkyawan fata ga miliyoyin ‘yan kasar Kongo da ke fama da nakasa, bayan ya kirkiri wasu mutum-mutumai masu aiki da kwakwalwar mutum wajen taimaka wa masu nakasar motsin labba.
Ya samar da wani mutum-mutumi da yake kwaikwayon ayyukan kwakwalwa, wanda yake shirin amfani da shi don taimaka wa masu fama da matsalar mutuwar barin jiki a Kongo.
Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo na da mutum miliyan 13 da ke fama da nakasa, kamar yadda alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Kongo suka nuna, kuma mafi yawansu sun samu nakasa a yaki, hatsarin mota ko wadanda aka haifa da nakasar.
Sedi bai dade da kammala digiri ba a sashen Injiniyacincin kwamfuta daga Jami’ar Fasaha da Sana’o’I ta Kinshasa.
A yayin da yake zaune a dakin gwaje-gwaje da bincike na jami’ar, ya bayyana yadda fasahar ke sanya mutum-mutumin yin aiki irin na mutum.
“Wannan injin na bayar da damar yin aiki irin na kwakwalwa ga mutum-mutumin da ke amfani da makamashin lantarki wanda ke isa ga rumbun kwakwalwarsa, sannan ya sauya zuwa sakon digital,” in ji Sedi yayin tattaunawar sa da TRT Afirka.
Kagaggun fina-finai
Fina-finan Hollywood ne suka ba shi kaimi, musamman shiri mai dogon zango na X-Men Evolution wanda a cikinsa Farfesa Xavier, babban jarumin shirin yake juya abubuwa daga kwakwalwar dan adam.
Ya ce “Tun ina karami, na kasance mai sha’awar Kirkirarriyar Basira…. Lamari ne da a ko yaushe yake jan hankalina kuma wannan ne bangaren da na so na yi fice a matsayi na na Injiniyan Kwamfuta. Na yi aiki sosai kan wannan tsawon shekara guda inda a watan Janairu na yi jarrabawar karshe.”
Sedi ya gamsu da cewa babu makura ga zurfin tunani, kuma akwai ayyuka da dama da za a yi game da alakar aiki tsakanin injina da kwakwalwa.
Bincikensa ya mayar da hankali kan rage yawan lokacin da ake dauka wajen bayar da horo ga abubuwa don amfani da gamayyar kwakwalwa-inji.
Tsarin da za a kyautata
Ya ce “Tunani da hakaito wani abu daga kwakwalwa ko zukatan mutane ya zama mai alakantuwa da sihiri a tsawon tarihi, saboda ba a haifar dana dam da irin wannan iko.”
Kalubalen Sedi na nan gaba shi ne rage girman abun da ya kirkira, habaka karfin aikin sa da ikonsa. Manufarsa ita ce ya fitar da wannan sabon abu ga jama’a.
Matashin da yake dan auta a tsakanin ‘yan uwansa hudu ya bayyana cewa yana samun kalubalen raba lokacin aikin samar da wannan fasaha da kuma lokacin aikin san a yau da kullum.
Yana bukatar aikinsa don samun na kai wa baki, sannan ua dauki nauyin wannan aiki nasa.
“Domin habaka bincike na, abun takaici ne yadda ban samu wani tallafi daga mahukuntan Kongo ba. Binciken kimiyya na ci gaba da neman kudin daukar nauyi a kasata, ya zama dole mu da kanmu a mu dauki nauyin wannan bincike,” in ji Sedi.
Jeab-Marie Beya, shugaban tsangayar Injiyanci a jami’ar Kinsasha na sa rai da fatan wannan aiki zai bayyana ingancin irin yadda ake bayar da horo a makarantar, duk da kalubalen da suke fuskanta.
Beya ya kara da cewa “Ina fada wa kaina cewa wadannan injiniyoyi sun gaji saboda yadda matakinsu ya yi girma idan aka kwatanta da abun da muke yi a cikin al’ummun Kongo. Zan so gwamnati ta taimaka mana ta yadda za mu kai ga gaji ko ma sama da yadda muke yi.”
Kirkira ga harkokin likitanci
Sedi ya kuma ce a yanzu haka a kasashen duniya ana habaka wannan inji mai kwakwalwa don amfanar ilimin likitanci, yawanci saboda maganin matsalolin illatar kwakwalwa.
‘Yan kasar Kongo da dama da TRT Afrika ta tattauna da su, sun bayyana cewa suna alfahari da Pierre Sedi kuma suna mamakin yadda ya kirkiri irin wannan aiki a Kongo.
“Ina matukar farin ciki da ganin dan kasar Kongo yana yin wannan aiki… Hakan na nuni da kasarmu na bunkasa a fannin fasaha da kere-kere”, in ji wani mazaunin Kinsasha.
Sedi ya ce ya ji dadi da mamakin irin yadda ‘yan kasar Kongo suke karfafa masa gwiwa ta hanyar nuna kishinsu ga aikin binciken da yake yi.
“Fatana shi ne na kafa wannan tsari a fannin likitanci ta yadda zai yi wa jama’a hidima musamma wadanda suke bukatar sa,” in ji Sedi.