Sarkin Beljiyom Philippe bai nemi afuwa saboda satar arziki, nuna wariya da aiyukan zaluncin da kasarsa ta yi a lokacin da take mulkin mallaka a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo. Amma ya zabi ya mika “zurfin nadamarsa” ga kaskantarwa da hukunci mai tsanani da aka dinga yiwa ‘Yan Kongo a lokacin mulkin mallaka.
Philippe jami’in gwamnatin Beljiyom na farko da shekaru biyu da suka gabata ya fito ya bayyana nadamar mulkin mallaka, kuma wasu ‘Yan Kongo na sa ran zai mika neman afuwar a hukumance a ziyarar farko da zaikai kasar tun bayan hawan sa mulki a 2013.
“Duk da cewa akwai ‘Yan aksar Beljiyom da yawa da suka nuna dattako, suka kaunaci ‘Yan Kongo sosai, shi kansa mulkin mallakar an yi shi ne don a sace dukiyoyi tare da yin mamaya”, Sarki Philippe ya fadawa zaman hadin gwiwa na majalisar dokoki a Kinshashan Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo.
“Wannan shugabanci ba shi da kama, bai dace ba, an yi zalunci da kisa, nuna wariya da kyama a cikinsa”.
Ya kara da cewa “Ya janyo aiyukan zalunci da kaskantarwa. A lokacin da nake ziyara ta farko a Kongo, a nan, a gaban ‘Yan Kongo wadanda har yanzu suke shan wahala, ina son na sake tabbatar da nuna tsananin nadamata ga wadannan abubuwa masu ciwo da aka yi.”
Duk da Sarkin na Beljiyom ya fara da tabo asalin mulkin malakar kasar, ba amfani da kalmar “Afuwa” ba, hakan ya bakantawa wasu da dama.
Ga wasu daga munanan bala’o’in da Beljiyom ta janyo a lokacin da take mulkin mallaka a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo.
Mutuwar ‘Yan Kasar Kongo miliyan 10
Wasu hasashe sun bayyana cewa, kisa, yunwa da annobar cututtuka sun janyo mutuwar ‘Yan kasar Kongo miliyan 10 a cikin shekaru 23 da Beljiyom ta mulki kasar daga 1885 zuwa 1960.
Sarki Leopold II ya yanki wajen da ya yi mulkin mallaka mai girma kilomita 100 a Dajin Tsakiyar Afirka inda yake cewa yana kare ‘jama’ar yankin’ daga Larabawa masu kama bayi.
Amma kuma ya fara kaddamar da munanan aiyuka a nahiyar ta Afirka.
A lokacin wannan mulkin mallakar, adadin jama’ar Kongo ya ragu da mutane miliyan 10.
Fyade da azabtarwa
Sarki Leopold II ya mayar da yankunan da yake wa mulkin mallaka sun zama sansanonin wahalarwa, ya samu arziki daga danyar roba da yake diba a yankin.
Roba ce ta habaka karfin tattalin arzikin kasar Beljiyom na kai tsaye.
Amma kuma wannan arziki da ya samu ba wai na albarkatun kasa da gona ba ne kawai, har da na bautar da dan adam.
Ta hanyar takurawa jama’ar yankin su samar da kaya da yawa, jama’ar Kongo sun rayuwa cikin matsi da zalunci inda har sai da aka bawa kowa aikin da zai yi.
‘Yan mulkin mallaka sun yiwa mutane da dama fyade tare da azabtar da su.
Guntile hannaye da kafafuwa
Sarki Leopold II ya yanke hannaye da kafafuwan mutanen da suke yi masa taurin kai, har da yara kanana da matan mazan da suka gaza biyan bukatarsa ta aikatau.
‘Yan mulkin mallaka na Beljiyom sun bayyana cewa, guntile gabbai ne hanyar da suke nuna suna sama da jama’ar Kongo.
Beijiyom ta yi amfani da mummunar hanya wajen yakar zanga-zangar nuna adawa da ake yi a lokacin inda aka takurawa sojojin Kongo da su yanko hannun duk dan tawayen da suka kashe, don a tabbatar ba a banza suka karar da makamai ba.
Danjarida Edmnd Dene Morel ne ya fara bayyana irin munanan laifukan Beljiyom, wadanda suka faro a 1885 a farkon karni na 20.
Morel ya yi babban kokari wajen yada irin abubuwan da Beljiyom ta aikata a yayin mulkin mallakar.
Ya bayyana hotunan yadda aka dinga takurawa mutane suna aikatau, kashe jama’a, yara da sojoji, mutanen da aka guntilewa hannaye da kafafuwa, azabtarwa da kisan kare dangi a Jihar Kongo.
A shekarar 2020, masu zanga-zanga sun karya mutum-mutumin Sarki Leopold II daga dandalin al’uma dake birnin Antwerp na Beljiyom a lokacin zanga-zangar gama-gari a duniya don nuna adawa da wariyar launin fata da mulkin mallakar Yammacin Duniya ya yi a baya.