An samu wani mai mukamin kanal a Jamhuriyyar Dimokuradiyar Kongo da laifin kisan kai da wasu laifuka da ke da alaka da kisan mutum 56 a lokacin da sojoji suka yi dirar mikiya kan masu zanga-zangar kin-jinin Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo.
Kanal Mike Mikombe ya kasance shugaban wani rukuni na soji a Goma, wanda a nan lamarin ya faru, na daga cikin sojoji shida da ke fuskantar shari’a.
Duk da cewa an yanke masa hukuncin kisa, sai dai an daina aiwatar da hukuncin, inda kawai ake yi wa mutum daurin rai da rai. Lauyansa, Serge Lukanga, ya ce zai daukaka kara kan wannan matakin.
Haka kuma akwai sojoji uku wadanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na shekara 10.
An ta zanga-zangar kin-jinin sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MONUSCO a bara, inda ake ta korafi kan cewa sun gaza kare farar hula.
A wata zanga-zanga da aka yi a watan Yulin 2022, sama da mutum 15 suka rasu, ciki har da masu aikin wanzar da zaman lafiya uku na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Goma da Butembo.