Daga Kudra Maliro
TRT Afrika, Kinshasa
Denis Mukwege, wanda likitan mata ne wanda ya taba lashe kyautar Nobel, na daga cikin mutum 22 da ke takarar shugabancin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a zaben da za a gudanar a ranar Laraba. Dan takarar dan shekara 68 ya bayyana cewa yana so ya ceto kasar wadda rashin tsaro ya addaba.
Yana daga cikin ‘yan takara sama da 20 wadanda ke son fafatawa da Shugaba Felix Tshisekedi wanda yake neman wa’adi na biyu.
Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo, ita ce kasar Afirka ta biyu mafi girma, tana fama da matsaloli na bukatar jin kai musamman a gabashin kasar inda dakarun gwamnatin kasar ke yaki da ‘yan tawaye wadanda suka raba sama da mutum milyan bakwai da muhallansu, kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yan Ci-rani ta Duniya ta bayyana.
Rikicin ya kashe miliyoyin mutane a sama da shekara 30 da aka kwashe ana yinsa. Sau daya aka taba mika mulki lami-lafiya a kasar a shekaru 60 da ta kwashe a matsayin kasa mai ‘yancin kanta.
Ana sa ran zabukan da ke tafe su kasance wadanda za su jawo dimokuradiyya ta dore.
Burin siyasa
Takarar da Dakta Mukwege yake yi ta zama shugaban kasa ba ta zo da mamaki ba, samakon an san shi a matsayin mutum ne da yake son siyasa da kuma sukar irin tsare-tsaren gwamnatocin baya da suka shude.
An fi sanin sa da Dakta Miracle, an taba ba shi kyautar Nobel a 2018 a tare da Nadia Murad ta Jamus.
An shaife shi a yankin Bukavu inda ya yi karatu a bangaren lafiya a Jami’ar Burundi, da Jami’ar Angers da ke Faransa da kuma Free University da ke Brussels inda a nan ya samu digirin-digirgir a 2015.
Yunkurin kisa
A watan Oktoba, wani abokin Mukwege ya cece shi daga masu kisa wadanda suka je gidansa dauke da makami a Bukavu.
Sai dai an kashe abokin nasa. “Na dauka za su kashe ni,” kamar yadda Mukwege ya shaida wa ‘yan jarida daga baya.
Babu tabbaci kan dalilin da ya sa suka yi niyyar kashe shi. A lokacin da yake kaddamar da yakin neman zabensa a watan Oktoba a wani dakin taro a Kinshasa babban birnin kasar, Mukwege ya bayyana cewa lokaci na kokarin kurewa domin ceto Kongo.
“Kasar mu ba ta tafiya da kyau. Ba za mu iya jira ba. Gobe lokaci ya kure,” in ji shi. A lokacin da ya bayyana hakan a Bukavu, lamarin ya biyo baya da tafi.
Sabon shiga siyasa
Duk da yadda aka san shi a duniya, masu sharhi kan siyasa na cewa shi sabon shiga ne a bangaren siyasa inda suka ce ba shi da magoya ba a kasa.
Yana daga cikin ‘yan bangaren adawa biyar wadanda suka tura wakilai domin tattaunawa kan yadda za a goyi bayan dan siyasa daya.
Sauran sun hada da Mosie Katumbi, tsohon dan takarar shugaban kasa Martin Fayulu da tsohon minista Augustin Matata Ponya da kuma Delly Sesanga.
Sai dai tattaunawar da aka yi a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu ba ta haifar da wani abin kirki ba duk da alkawura da aka yi a tsakaninsu.