Hanya ce ta samun makamashi mai tsafta da kuma takin zamani wanda zai dinga kyautata rayuwar yau da kullum ta jama’ar Kongo, da kuma habaka tattalin arzikin kasar.
A lokacin da Destin Babila, matashi mai sana’ao’i daga garin Pointe-Noire, ya gabatar da shirinsa na Bipchar da abokansa a 2019, sai aka fara tantama da kokwanto.
Ya tunatar da cewa “Bakaken maganganu mafiya tsafta ma an fade su ne labaran ban dariya da ke kaskantarwa ko ma karya gwiwa,”. “Me za mu iya samu daga bola? Bola dai bola ce” ---
“Amma kuma,” Desbin Babila ya mayar da martani cikin fashewa da dariya, “gaskiyar na nan: Akwai zinariya a bola. Koriyar zinariya ce”.
Bayan shekaru uku, sai mafarkin ya dauki salo sannan masu tantama suka rikice. Tare da iskar Wumela, abun da mai sana’a ya kirkira, sai ga shi bola na fuskantar sabuwar rayuwa ta biyu, na habaka. Tare da gawayin da aka samar da ake kira, bio-charcoal ko biochar, sannan takin zamani ma na nan. Wadannan ne kayan farko da aka samar, wanda sua dauki ma’aikata na dindin guda 12.
Gawayin zamani
Ya yi mamaki da farko, Destin Babila ya bayyana ya yi mamakin irin bola da sharar da ake fitarwa daga garin Pointe-Noire.
“Kaso 80 na bolar ana amfani da ita don samar da wasu abubuwan” inji Destin Babila. “Mun yi mamakin yawan bolar dake kewaye da mu. Mun kaddamar da shirin ne don sake habaka bola tare da samar da makamashin mai tsafta ga al’uma.”
Wannan makamashi mai tsafta shi ake kira biocharcoal, sannan ana samar da takardun aiyukan ofis, kayan noma, da ma wasu kayayyakin da ake amfani da sy a gidajen jama’a.
Domin samun gawayin biochar, ma’aikatan Wumela suna tattara bola nau’i daban-daban. Sai a busar, gasawa sannan a nike ta don a samu bakar toka da take manne. Sai a zo a kuma mulmula su don samar da gawayin da ake so. Bayan an busar da su na tsawon kwanaki uku, sai a fara amfani da shi. Wannan aiki na samar da gawayin dan adam, wata babbar hanya ce ta kare dazuka da bishiyu.
Kiyaye dazuka da tsare su
A wanii nazari da Bankin Duniya ya yi a madadin COMIFAC (Hukumar Kula da Dazukan Tsakiyar Afirka) a shekarar 2013, an gano yadda samar da gawayi yake yin babbar narazana ga dazukan yankin. Rahoton ya bayyana cewa, idan har za a ci gaba da yadda ake yi, samar da gawayi ne zai zama barazana mafi girma da hatsari ga Kogunan Kongo a shekaru masu zuwa, inda ake kara samun sare bishiyu. Hasashen da aka yi ya bayyana cewa sama da kaso 90 na katakon da aka diba daga Dazukan Kongo a a samar da gawayi ne da su, kuma kowanne mutum guda na bukatar kyubikmita daya a kowacce shekara.
Destin Bibila ya fadi cewa “Ka gani, duba da alkaluman da aka fitar a hukumance, a 2016 a kasata ta Kongo, muna amfani da tan dubu 100,000 na gawayi, da kuma kusan tab 132,000 itace. Hakan na nufin idan muka yi kokari, za mu iya yakar sare dazuka da hana gurbatar yanayi.”
Gawayin Biochar na taimakawa wajen yaki da sauyin yanayi
Kari ka iskar da dan adam ke samarwa ta bio-carbon, wannan sabon abu na ta samar da biochar, sannan an fara samar da takin zamani daga bola domin amfanin manoma.
“Sinadarin pyrolysis ne ke kona bolar da ake tarawa, a wani akwakun dfuwa na musamman, da ake hura masa wuta sama da daraja 300 ba tare da shakar iska ba. Dole ne ya zama muna da carbon da kaso 80.” Inji Destin Babila.
Wannan sabon takin na zamani na da matukar muhimmanci ga harkokin noma
“Babbar manufar samar da gawayin Biochar ita ce don a habaka kasa, a wanzar da rayuwa da albarkarta. Yna sanya kasa ta dinga rike a kalla kaso 15 na ruwanta, sannan da kula da acid din dake cikin ta. Yana sanya kasa ta rike carbon dioxide da yawa wanda hakan na taimakawa wajen yaki da dumamar yanayi a duniya. Idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata, gawayin baiochar zai iya habaka amfanin gona da kaso 50 cikin 100,” inji Destin Babila
Wadannan bayanai sun dace da kalaman kwararru daga Pro Natura, Kungiyar Kasa da Kasa da aka samar a Barazil bayan taron Rio 1992. Manufofinta su ne: “habaka karkara, kare tsirra da kuma yaki da dumamar yanayi a kasashe masu tasowa.”
“Kaddamar da gram 300 zuw akilo 1 na gawayin biochar a duk fadin sukwayamita daya zai habaka albarkar amfanin gona a kasashe masu zafi da kaso 50 zuwa 200, kamar yadda shafin yanar gizon kungiyar ya bayyana. Zuba takin sau daya na samar da haihuwar tsirrai na tsawon lokaci, da kuma tsotse carbon wanda ke taimaka wajen yaki da dumamar yanayi. An yi nazari a kimiyyance kan tasirin gawayin biochar.,
- Karfafa haihuwar kasa (da kaso 40)
- Habaka rike sinadaran gina jigi (Da sama da kaso 50).
- Yana kara karfin kasa wajen rike ruwa (Har zuwa kaso 18)
- Yana karawa kasa yawan PH (Matsakaici sama da maki 1).
- Yana kara sanya kasa ta zama ta asali da hana ta gurbata
- Yana rage fitar da iskar N20 da CH4
Alkawarantawa duk da akwai komai
Babban kamfani a Kongo na bibiyar bunkasar gawayib biochar. Ya mayar da hankali wajen “samar da muhalli ingantacce”, wannan kamfani na son hatsi ya zama ana sarrafa shi ta hanya mafi inganci da dacewa da muhalli. Kamar yadda kwararre a wannan fanni ya bayyana.
“Ana ci gaba da gwaje-gwaje kuma za öu yanke hukunci a karshen al’amarin.”, a kaulin wani babban jami’i na wannan kamfani.
Mai habaka iskar carbon ta dan adam ta Wumela ya ce “Ya yi kokarin bayar da gudunmowa wajen habakar aiyukan noma a Kongo, godiya ga biochar.” Babban kalubalen da ake fuskanta kawai shi ne rashin isassun kudade. Destin Babila ya ce “Har yanzu da namukudaden muke aiki, kuma ba mu iya biyan bukatar da ake da ita ba wadda a kullum karuwa take.”
Sakamako, ana iya samar da tan 30 ne kawai a kowanne wata...
“A Turai, suna da isassun kudade, amma ba su da bola. A nan kuma muna da bola, amma ba mu da kudade”, inji Destin Babila.