Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati EFCC ta ce ta kama ‘yan kasar China 13 kan zargin gudanar da ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Jihar Kwara da ke tsakiyar kasar.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Twitter ta ce “Jami’an hukumar EFCC na shiyyar Ilorin sun kama ‘yan kasar China 13 bisa laifukan da suka shafi hakar ma’adinai ba a kan doka ba.
“Wannan laifi ne da sashe na daya karamin sashe na 8 na kundin tsarin mulkin kasar na 1983 ya ayyana a matsayin laifin da za a hukunta mutum a kansa,” a cewar sanarwar.
EFCC ta ce mutanen sun hada da maza 12 da mace daya, kuma an kama su ne a ranar Laraba 12 ga watan Yulin a yankin unguwar rukunin gidajen gwamnati wato GRA a Ilorin.
“An kama su ne bayan samun bayanan sirri a kan ayyukan da suke yi da suka hada da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da kin biyan haraji ga Gwamnatin Tarayya kamar yadda doka ta tanada,” in ji EFCC.
Mutanen suna hada da ‘yan shekara 26 zuwa 53.
Aiki ba bisa ka’ida ba
EFCC ta ce kafin kamen nasu, binciken da aka gudanar kan ayyukan da suke yi ya hada da mallakar wurare daban-daban da suke hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a kusan dukkan kananan hukumomi 16 na jihar.
“A yayin da ake tuhumarsu, mutanen sun amsa cewa su ma’aikatan wani kamfanin China ne mai suna W. Mining Global Service Limited da ke Olayinka a karamar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.
“An gano cewa kamfanin na amfani da giranayit ba bisa ka’ida ba don samar da tayil yana sayarwa a cikin Nijeriya.”
EFCC ta kuma ce bincike ya sake gano cewa wasu daga cikin mutanen da ake zargin da ke aiki a kamfanin ba su da takardar izinin yin aiki a kasar, sun shiga Nijeriya ne kawai da bizar masu ziyara.
EFCC ta ce da zarar ta kammala bincike za ta mika mutanen ga kotu don yin shari’a.
Yawaitar hakar ma’danai ba bisa ka’ida ba
Ko a makon jiya sai da shugaban EFCC Abdulkarim Chukkol ya koka kan ayyukan hakar ma’dinai ba bisa ka’ida ba a Kwara, a yayin wani taron horar da ‘yan jarida da ya halarta.
Chukkol ya bayyana haka da cewa mummunar barzana ce ga tattalin arzikin jihar da na kasa baki daya.
Hukumar EFCC shiyyar Ilorin ta kama akalla masu ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba 80 a wata takwas da suka wuce da kuma tirela 24 makare da ma’adinai daban-daban.
Sannan a watan Satumban 2022 ma EFCC shiyyar Ilorin ta kama wani dan China Dang Deng, shugaban kamfanin Sinuo Xinyang Nigeeia Ltd da tan 25 na danyen ma’dinai inda aka gurfanar da shi a gaban wata Babbar Kotu a Ilorin ran 19 ga watan Oktoban 2022.
Hukumar ta yi gargadin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba a yakin da take yi da cin hanci kuma ba za ta bar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida su ci karensu babu babbaka a kasar ba.