Hukumomin Jami’ar Abdulmumini da ke Nijar sukan ba shi dama don ya koyar da ɗalibai abubuwan da suka shafi kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe da ma tarihin kiɗe-kiɗe.
Mawaƙin wanda ake yi wa laƙabi da Adumulmula ya fara yin fice ne a shekarar 2009, bayan da ya fitar da wani sabon kundinsa na waƙoƙi wanda ya samu karɓuwa sosai a lokacin. Sannan fitaccen mawaƙin ya bayyana wa TRT Afrika Hausa dalilin da ya sa ya koyi kiɗan gurmi.
