Mawaƙa na daga cikin masu ƙawata harkokin siyasa a Nijeriya, kuma suke bayar da gudunmawa wajen tallata 'yantakara, har su isar da manufofin 'yantakarar ga saƙo da lunguna waɗanda su 'yantakarar ba za su iya shiga su kai ba.
A fagen siyasa, mawaƙan kan rera waƙoƙin da suke ɗaga darajar 'yantakara waɗanda suke shiga bakin jama'a kuma suke mayar da 'yantakarar fitattu har ma a faɗin ƙasa.
