Akalla mutane 47 ne suka mutu, yayin da wadansu 22 suka samu raunuka bayan wani hari da kungiyoyin 'yandaba suka kai a cikin dare a wata unguwa da ke kusa da babban birnin kasar Haiti, wato Port-au-Prince, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta bayyana a ranar Litinin.
Kungiyoyin 'yan aba ne ke iko da kusan kashi 70 cikin dari na birnin Port-au-Prince, kuma rikicin wadannan kungiyoyi masu dauke da makamai ya tilastawa mutane miliyan 1.5 gudun hijira a fadin kasar, a cewar MDD
