A Nijeriya ana yawan samun rahotannin Kisan Rubdugu (Mob Killing), inda gungun mutane kan far wa wanda aka zarga da aikata laifi, har su kan kassara shi ko su yi masa kisan gilla, duk da cewa shari’a babu wanda ta bai wa haƙƙin yankewa ko zartar da hukunci idan ba kotu ba.
Masana shari’a da zamantakewa sun ce Kisan Rubdugu mummunar ɗabi'a ce da ke saurin gurɓata zamantakewar al'umma da haddasa fitina, tare da kawar da aminci da tausayi, ko da kuwa masu aikatawar suna da kyakkyawar niyyar ganin an hukunta mai laifi. Ga rahoto na musamman kan illolin wannan baƙar halayya.


Ƙarin Bidiyoyi
Illar kisan rubdugu a zamantakewar al'umma
Masana shari’a da zamantakewa sun ce Kisan Rubdugu mummunar ɗabi'a ce da ke saurin gurɓata zamantakewar al'umma da haddasa fitina, tare da kawar da aminci da tausayi, ko da kuwa masu aikatawar suna da kyakkyawar niyyar ganin an hukunta mai laifi.
Ƙarin Bidiyoyi