Batun dawo da tallafin man fetur a Nijeriya ya sake raba kan manyan 'yan takarar shugaban ƙasa a ƙasar a 'yan kwanaki nan, tun bayan kalaman Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC da ya bayyana cewa idan an zaɓe shi zai dawo da tallafin.
Sai dai Shugaba Tinubu na jam'iyyar APC da ya cire tallafin a 2023 ya soki Atiku kan wannan kalamai, yana mai cewa ya faɗi haka ne saboda a zaɓe shi, yayin da shi ma Peter Obi na jam'iyyar NDC ya bayyana cewa yana goyon bayan tallafin, kuma ba zai cire shi ba idan aka zaɓe shi.
Ku kalli bidiyon nan sannan ku bayyana mana ra'ayinku.
