Matashiyar nan 'yar Jihar Gomba a arewa maso gabashin Nijeriya, Maryam Ibrahim Dan Azumi wacce ta lashe Musabaƙar Karatun Alƙur'ani ta Duniya ɓangaren mata da aka gudanar a Saudiyya inda ta wakilci Nijeriya, ta bayyana sirrin nasararta a wajen musabaƙar.
Maryam, wacce a yanzu haka take aji huɗu a jami'a ta kuma bayyana wa TRT Afrika Hausa irin horon da suke samu a gida wajen haddar Alƙur'ani. Shekaru biyu da suka wuce yayarta Hajara Ibrahim Dan Azumi ta lashe Musabaƙar Alƙur'ani a ƙasar Jordan inda ta wakilci Nijeriya.
