Tawagar ƙwallon ƙafar Ireland, wadda ke goyon bayan Falasɗinawa, ta lallasa Isra'ila da ci 3-0 a Gasar UEFA. Tun da farko an yi ta kiraye-kiraye ga Ireland ta ƙaurace wa wasan bayan an zargi Isra'ila da yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza, amma daga bisani Ireland ta shiga wasan bayan UEFA ta ƙi amincewa da waɗannan kiraye-kiraye.
A lokacin soma wasan, 'yanwasan Ireland sun ƙi yin musabaha da takwarorinsu na Isra'ila sannan sun ɗaura baƙaƙen ƙyallaye domin nuna alhininsu ga Falasɗinawa da Isra'ila ta kashe.
