An kawo akwatin gawar marigayi Jagoran Addinin Iran, Ali Khamenei, wanda aka kashe a wani harin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila, zuwa bikin bankwana a babban birnin Tehran, inda wakilan kasashen duniya za su halarci bikin.
Bikin na ranar Juma'a zai samu halartar dubban iyalan wadanda aka kashe a yakin Amurka da Isra'ila kan Iran, wadanda suka taru don yin jimami kusa da wurin bankwanan.
An kashe Khamenei a wani harin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wani lamari da ya haifar da yakin makonni da kuma kara ta'azzara rikici a Gabas ta Tsakiya.
A cewar jadawalin jana'izar da aka sanar, za a gudanar da wani bikin tunawa da Khamenei a hukumance a ranar Juma'a, tare da halartar shugabannin kasashe, manyan jami'ai da shugabannin addinai.
Leaders, senior officials or representatives from more than 30 countries, including Russia, China, Pakistan, India, Tajikistan, Georgia and Cuba will attend the ceremony, Iranian media reported.
Shugabanni, manyan jami’an gwamnati, ko wakilai daga sama da kasashe 30 - ciki har da Rasha, China, Pakistan, India, Georgia da Cuba - ne za su ahalrci taron, in ji kafafen watsa labarai na Iran.
Pakistan, wacce ita ce babbar mai shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran kan kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya, ta ce Firaministanta Shehbaz Sharif zai halarci jana'izar da za a yi a Tehran ranar Asabar.
Kasashen China, Afghanistan da makwabtan Iran a yankin Caucasus sun ce za su aika wakilai.
Hotunan da aka buga a yanar gizo ta kafofin watsa labaran gwamnatin Iran sun nuna Janar Ahmad Vahidi yana halartar wani taro game da jana'izar Khamenei, mai shekaru 86, sannan ya zauna kusa da akwatin gawarsa.
Vahidi, wanda ke jagorantar rundunar kare juyin juya halin Iran, ya zama babban mai taka rawa wajen tsara tsauraran matakan Iran na tattaunawa kan yiwuwar kawo karshen yakin har abada da Amurka, in ji masana.
Ana kyautata zaton yana cikin wata karamar kungiya da ke hulda kai tsaye da sabon Shugaban Koli na Iran Mojtaba Khamenei, wanda ba a gan shi a bainar jama'a ba bayan an ruwaito cewa ya ji rauni a hare-haren Amurka da Isra'ila na ranar 28 ga Fabrairu wanda ya kashe mahaifinsa, Khamenei babba.
Ba a ga Vahidi da kansa a bainar jama'a ba tun ranar 8 ga Fabrairu, makonni kafin fara yakin.
'Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a'
Za a ci gaba da gudanar da bukukuwan bankwana a Tehran a ranakun 4 ga Yuli da 5 ga Yuli, sannan a yi babban taron jana'izar a babban birnin a ranar 6 ga Yuli.
Sannan za a mayar da bukukuwan jana'izar zuwa birnin Qom mai tsarki a ranar 7 ga Yuli.
A ranar 8 ga Yuli, an shirya bukukuwa a Iraki, ciki har da Baghdad, Najaf da Karbala, inda manyan mutane na addini da siyasa za su karbi gawar sannan a kai ta manyan wuraren ibada na Shi'a.
An shirya gudanar da jana'izar karshe da binne gawar a ranar 9 ga Yuli a wurin ibada na Imam Ali Reza da ke arewa maso gabashin birnin Mashhad, daya daga cikin wurare mafi tsarki na Shi'a.
"Yawan jama'a da suka halarci jana'izar shugaban da sauran wadana aka kashe, a zahiri, zai zama wata kuri'ar raba gardama ga Jamhuriyar Musulunci," in ji jagoran addu'ar Juma'a na Qom Ayatollah Mohammad Saidi ga kafofin watsa labarai na gwamnati.
Ana sa ran bukukuwan za su jawo mutane miliyan 15 zuwa 20 masu makoki, a cewar jami'ai, wanda hakan zai sanya ya zama jana'izar gwamnati mafi girma a tarihin kasar.
Kisan Khamenei, da kuma gadarsa da dansa Mojtaba ya yi a matsayin shugaban koli na uku a Iran, a yakin da ya yi da manyan abokan gaba, ya nuna wani lokaci mai tsawo a cikin shekaru 47 da suka gabata a Iran.
A halin yanzu, Iran da Amurka sun kammala tattaunawa kai tsaye a Doha, in ji masu shiga tsakani a ranar Alhamis, yayin da suke ci gaba da kokarin ci gaba da tattaunawa da rage tashin hankali bayan musayar wuta a kwanan nan.
A watan Yuni, Washington da Tehran sun amince da yarjejeniyar fahimtar juna, wacce Pakistan da Qatar suka shiga tsakani, wacce ta hada da tsagaita wuta na kwanaki 60 don dakatar da yakin da ya barke da hare-haren Amurka da Isra'ila a karshen watan Fabrairu, da kuma sake bude mashigar Hormuz da aka rufe.
Yarjejeniyar mai matakai 14 ta kuma sanya jadawalin tattaunawa don kawo karshen yakin har abada da kuma warware batutuwa kamar shirye-shiryen Hormuz, kudaden sake gina Iran da kuma makomar shirin nukiliya na Tehran.








