| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
5 minti karatu
Miliyoyin mutane sun halarci jana’izar Khamenei a Tehran
Masu jimami sun yi tattaki a tituna suna ɗaga tutocin Iran da na ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, da kuma jajayen tutoci da ke nufin ɗaukar fansa.
Miliyoyin mutane sun halarci jana’izar Khamenei a Tehran
Taron ya ba wa Iran damar bayyana tirjiya bayan makonni biyar na yaki da Amurka da Isra'ila / AFP

Ɗimbin jama’a sun halarci jana'izar Jagoran Addinin Iran Ali Khamenei a Tehran a ranar Litinin, inda hukumomi suka ƙiyasta cewa miliyoyin mutane sun hau kan tituna, adadin da zai iya wucewa ko yin gogayya da na waɗanda suka halarci jana’izar wanda ya gada kusan shekaru arba'in da suka gabata.

Hukumomin ba su bayar da adadin waɗanda suka fito a hukumance ba, amma hotunan da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ɗauka sun nuna adadi mai yawa a kan manyan tituna a babban birnin Iran.

Jimamin ya bai wa Iran damar nuna juriya bayan makonni biyar na yaƙi da Amurka da Isra'ila, ko da yake har yanzu ana mayar da hankali kan magajin Khamenei, ɗansa Mojtaba Khamenei, wanda bai bayyana a bainar jama'a ba tun lokacin da ya fara jagoranci.

Bayan kwana biyu a gidan sarauta na Tehran, gawar Khamenei, wanda aka kashe a ranar farko ta yaƙin Gabas ta Tsakiya a ranar 28 ga Fabrairu, ta fara tafiya a babban birnin tare da ɗimbin jama'a.

Furanni sun rufe akwatin gawar yayin da take kan tituna, kamar yadda hotunan AFP suka nuna.

Hukumomi suna fatan guje wa sake afkuwar hatsaniyar da ta afku a lokacin jana'izar magabacin Khamenei, Ruhollah Khomeini a shekarar 1989, wadda kimanin mutane miliyan 10 suka halarta, a cewar kamfanin dillancin labarai na IRNA.

Dandazon jama'ar da suka taru a lokacin bankwana da Khomeini ya yi ajalin mutane sama da 10 tare da jikkata sama da 10,000.

"Idan zan kwatanta wannan jana’iza da waccan, zan iya cewa ba su bambanta ba kwata-kwata. Amma taron jama'a a wannan karon ya fi nuna damuwa," in ji Gholamreza Khanbabaei, mai shekaru 58, wadde ta halarci taron.

An rufe sararin samaniyar Tehran a ranar Litinin yayin da ƙasar ke tsaye cak domin tunawa da tsohon shugaban.

Masu makoki sun yi tattaki a tituna suna ɗaga tutocin Iran da kungiyar Hezbollah ta Lebanon, da kuma tutocin ja da ke nuna ramuwar gayya.

Wasu sun taru a dandalin Imam Hussein da ke gabashin Tehran inda suka rataye hoton shugaban Amurka Donald Trump, a cewar kafofin watsa labaran gwamnati.

An ga tsohon shugaban ƙasa Mahmoud Ahmadinejad yana halartar jerin gwanon, a cewar kafofin watsa labaran cikin gida.

A cikin tsananin zafi, manyan motoci sun fesa wa masu makoki ruwa don sanyaya su, yayin da masu shirya taron suka rarraba tutocin Iran da hotunan Ali da Mojtaba.

Mojtaba bai halarci taron ba

Hanyar da aka bi ta zagayen ta kai tsayin kimanin kilomita 20 (mil 12).

Kwana daya kafin hakan, dubban mutane sun cika babban birnin Mosalla domin girmama Khamenei da iyalansa huɗu da aka kashe a hare-haren sama na Isra'ila, waɗanda an kai su ne bisa dogaro ga bayanan sirri na Amurka.

Manyan ganuwar kankare a harabar sun yi iyaka tsakanin jama'a da akwatin gawar don hana cinkoso da turmutsutsu.

Ba a san matakin kusanci da jama'a za su samu a lokacin taron na ranar Litinin, amma hukumomi sun san cewa a shekarar 1989 an tilasta musu amfani da jirgin sama mai saukar ungulu don daukar Khomeini zuwa wajen binne shi bayan masu makoki sun afka wa motarsa, lamarin da ya sa rigar jana'izarsa ta yage kuma gawarsa ta fadi kasa.

Taron ranar Litinin zai biyo baya da irin wannan lamari a cibiyar malamai ta Qom a ranar Talata da kuma a biranen Najaf da Karbala masu tsarki na Iraki a ranar Laraba, wanda daga nan za a yi jana'izar Khamenei a garinsu na Mashhad a arewa maso gabashin Iran a ranar Alhamis.

'Ya'yan Ali Khamenei uku sun yi wata gagarumar bayyana a bainar jama'a a ranar Lahadi, wanda hakan ya kara nuna rashin kasancewar Mojtaba, wanda aka nada a matsayin shugaban addini jim kadan bayan kisan mahaifinsa amma har yanzu bai bayyana a bainar jama'a ba.

Jami'ai sun ce ya ji rauni a hare-haren sama amma har yanzu ba a san irin raunin da ya samu ba. Sabon kwamandan dakarun juyin juya hali na Iran, Ahmad Vahidi, wanda aka kashe wanda ya gada a ranar 28 ga Fabrairu, shi ma ya bayyana a jana'izar a karo na biyu a ranar Lahadi, a wannan lokacin a bainar jama’a, bayan da aka daina ganin sa tun lokacin yaƙin.

'Ɗaukar fansa'

Gwamnati na sha'awar yin kira ga jama'a da su goyi bayan hukumomi bayan zanga-zangar da aka yi a watan Janairu wanda ƙungiyoyin kare hakkin ɗan’adam suka ce an dakatar da shi ta hanyar wata murƙushewa da ta kashe dubban mutane.

Yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran ya tsaya cak bayan tsagaita wuta da kuma yarjejeniyar farko da aka cim ma da Amurka. Amma Washington da Tehran sun yi gargaɗin cewa a shirye suke su ci gaba da ɗaukar matakin soji, kuma ɗaukar fansa ya kasance babban jigo a jana'izar.

Wasu daga cikin magoya bayan Khamenei a dandazon jama’ar na ranar Litinin sun maimaita wannan saƙon.

"Muna son ɗaukar fansa. Dole ne a yi hakan. Domin daga baya, idan ba a yi hakan ba, zai ƙara ta'azzara lamarin," in ji Khanbabaei.

Rumbun Labarai
Sojin ruwan Amurka takwas sun jikkata a harin makami mai linzami da Iran ta harba a Mashigar Hormuz
Erdogan: Yarjejeniyar Makka ba ta da manufa a kan Iran ko Isra’ila
Ƙungiyar yarjejeniyar tsaro ta Makka ta tattauna kan yin taron gaggawa don tallafa wa Saudiyya
Abbas ya yi gargaɗin cewa manufofin Isra’ila na barazana ga wanzuwar Falasdinu
Iran ta yi tayin sake buɗe Mashigar Hormuz cikin kwanaki bakwai idan Amurka ta sassauta matsin lamba
Birtaniya za ta bai wa Saudiyya 'kariyar' soji don daƙile hare-haren 'yan Houthi
Amurka ta ce za a dakatar da zirga-zirgar dukkan kamfanonin jiragen saman Iran a duniya daga Laraba
Qatar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran
Dalilan da suka sanya Netanyahu yunƙurin hana jam’iyyun Larabawa shiga zaɓe a Isra'ila
Yaƙin Amurka da Iran ya laƙume $150B na tattalin arzikin ƙasashen Larabawa a cikin wata guda: MDD
Amurka ta hana shugaban Falasɗinawa bizar halartar Babban Taron MDD a karo na biyu
Kungiyar OIC ta yi Allah wadai da hare-haren 'yan Houthi a Makka da yankin Madina
Yaƙin Yemen ya raba fiye da mutum 100,000 da muhallansu — Majalisar Ɗinkin Duniya
Iran ta ba da umarni a yi shirin yaƙi da tsagaita wuta da yanayin bayan yaƙi ga dukkan ƙasar
Hukumar sa ido kan Pentagon ta ce yaƙin Iran ya jawo ƙarancin makamai 'masu mahimmanci'
Saudiyya ta ce wasu jirage marasa matuƙa da aka aika daga Iraƙi sun kai hari kan wani bututun mai
Amurka ta yi biris da kiran Saudiyya na kai wa Houthi hari, ta ce za ta ba da taimakon bayanan sirri
Isra’ila ta sake jaddada barazanar kai hari wuraren makamashin Iran
Ƙin amincewar Ingila da mamayar da Isra’ila ke yi ba bisa doka ba ya kawo babban sauyi- Wani Malami
Trump ya ce Amurka tana samun nasara a kan Iran kuma za ta kira Mashigar Hormuz da 'Mashigar Trump'