| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya za ta rage farashin man fetur tsawon kwanaki 30
Sai dai Ministan Kuɗin Ƙasar Taiwo Oyedele ya ce ragin farashin ba wai tallafi ba ne, amma wani shiri ne na gwamnati na sayar da mai a farashi mai sauƙi.
Gwamnatin Nijeriya za ta rage farashin man fetur tsawon kwanaki 30
Gwamnatin Nijeriya ta ce za a rage farashin ne tsawon kwanaki 30 a karon farko

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da wani mataki na rage farashin mai zuwa kimanin naira 1,350 a kan kowace lita, tana roƙon masu tace mai da masu shigar da shi ƙasar da shi su jure wa sauyin na ɗan lokaci.

Ministan Kuɗin Ƙasar Taiwo Oyedele wanda ya bayyana haka ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Abuja, ya ce matakin ya zama dole sakamakon yadda farashin mai ya ƙaru, abin da ya haifar da hauhawar farashin mai a duniya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

"Za mu sauƙaƙa farashin man fetur da NNPC Limited ke rabawa tsawon kwanaki 30 masu zuwa a karon farko, tare da bayar da fifiko ga motocin haya a duk faɗin ƙasar," in ji Ministan.

Sai dai ministan ya ce ragin farashin ba wai tallafi ba ne, amma wani shiri ne na gwamnati na sayar da mai a farashi mai sauƙi.

Haka kuma gwamnatin ta ce ana tunanin ci gaba da sayar da ɗanyen mai ga masu tace mai na cikin gida don rage matsalar hauhawar farashin a kasuwannin mai na duniya.

Ya ce gwamnati za ta ɗauki ƙarin wasu matakan saboda matakan da ake da su yanzu ba sa magance matsin lambar da magidanta da ‘yankasuwa suke fuskanta ba, wadanda ake fama da su sakamakon ƙaruwar farashin man fetur.

Minista Taiwo ya ce za a ringa sake yin duba kan farashin a duk wata.