An kashe aƙalla mutane 28 a sabbin hare-hare da ‘yanbindiga suka a ƙananan hukumomi uku na Jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya, duk da dokar hana fita daga yamma zuwa safiya da gwamnatin jihar ta sanya a watan jiya domin daƙile matsalar rashin tsaro.
Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Ƙaramar Hukumar Mangu da Bokkos da kuma Barkin Ladi, waɗanda suka fuskanci jerin hare-hare a baya bayan nan, lamarin da ya ƙara jefa mazauna yankunan cikin fargaba tare da kawo cikas ga ayyukan noma da kiwo da kuma sauran harkokin tattalin arziki.
Rahotanni sun bayyana cewa, sabon harin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi a Ƙaramar Hukumar Jos South, inda aka kashe Fulani makiyaya biyu tare da jikkata mutum shida a harin da wasu 'yanbindiga suka kai kan motarsu a kusa da wani gidan mai da ke Bukuru.
Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da harin, inda ya bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna dawowa ne daga kasuwar shanu lokacin da aka kai musu hari da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
Babayo ya yi Allah wadai da harin tare da yin kira ga jami'an tsaro da su gano waɗanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban a kotu.
Kazalika ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti, yayin da “har yanzu ba a san inda mutum ɗaya yake ba.”
Haka kuma sabon harin ya faru ne ƙasa da makonni biyu bayan wani hari da aka kai kan makiyaya a kusa da garin Kassa da ke Barkin Ladi, inda aka kashe mutane biyar tare da jikkata wani mutum guda, kamar yadda jaridar Daily Trust a Nijeriya ta rawaito.
Hare-hare duk da dokar hana fita
Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita a ranar 21 ga Satumba bayan taɓarɓarewar tsaro a Mangu, da Bokkos da kuma Barkin Ladi.
Dokar, wadda ke aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, an sanya ta ne domin bai wa jami'an tsaro damar shawo kan matsalar tsaro tare da kare rayukan mazauna yankunan. Hukumomi sun kuma hana amfani da babura a yankunan da abin ya shafa.
Sai dai duk da wannan mataki da aka ɗauka an ci gaba da samun rahotannin hare-hare tun bayan fara aiwatar da dokar.
An samu rahotannin kashe mutane da dama, ciki har da mata da yara, yayin da aka lalata gidaje da gonaki tare da kashe dabbobi a watan Satumba, haka kuma rikicin ya tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu.
Ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton, rundunar 'yansanda da jami'an soji ba su fitar da wata sanarwa kan wannan sabon harin ba.



















