| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta musanta ɗora wa Masar laifin rikin Ethiopia bayan ƙin yardar Alƙahira
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta ce tana ba da muhimmanci na musamman ga dangantakarta ta Masar, tana mai bayyana ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin mambobin da suka kafa ƙungiyar.
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta musanta ɗora wa Masar laifin rikin Ethiopia bayan ƙin yardar Alƙahira
Hukumar ta sake atbbatar da jajircewarta ga 'yancin kan iyakan ƙasashe mambobin Ƙungiyar Tarayyar Afirka. / AU

Ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU ta ce ba ta so ta ɗaura wa Masar ko kuma wata ƙasa maƙwabciya laifi game da abin da ke faruwa a cikin ƙasar Ethiopia ba bayan Alƙahira ta ƙi yarda da wata sanarwar da ƙungiyar ta fara fitarwa game da rikice-rikicen yanki.

AU ta ce ta gane ƙin amincewar Masar ga sanarwarta ta ranar 1 ga watan Oktoba, wadda ta yi kira ga Ethiopia da Eritrea da kuma Masar su kai zuciya nesa sosai da barin ƙofofin tattaunawa a buɗe da sasanta matsalolinsu ta hanyar diflomasiyya.

“Babu wani yanayin da sanarwar ta yi niyyar ɗora alhakin abubuwan da ke faruwa a Ethiopia kan wata ƙasa maƙwabciya, in ji hukumar.

Ta ce kiran ya zo ne bayan an kori jami’an diflomasiyya daga Addis Ababa da Alkahira da Asmara kuma an yi shi ne domin hana rashin jituwa da taɓarɓarewar ko kuma faɗaɗa tashin hankali da zai iya barazana ga zaman lafiyar yankin.

Goyon bayan ‘yancin kan iyakoki

AU ta kuma sake tabbatar da jajircewarta ga ‘yancin kai da ‘yancin kan iyakoki da haɗin kan ƙasashe mambobinta tare da ƙa’idar rashin katsalandan a cikin harkokin cikin gidansu.

Ya jaddada cewa sanarwar ta faɗa ne kacokan cikin aikinta na inganta zaman lafiya da tsaro da lumana kuma ba ta da niyyar tsokaci kan ababen da ke faruwa a cikin ƙasashe mambobinta.

Masar ta ƙi amincewa ne da sanarwar hukumar ranar Asabar, inda wata majiya a hukumance ta bayyana ta a matsayin wani “yunƙuri da baza a iya ganewa ba” na shigar da Alkahira cikin wani lamarin cikin gida na Ethiopia.

Hukumar Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta ce tana ba da muhimmanci na musamman ga dangantakarta da Masar, tana mai bayyana ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka kafa ƙungiyar da kuma wata muhimmiyar ƙawar aiki wajen inganta zaman lafiya da tsaro da haɗin kai da ci-gaba a faɗin Afirka.


Rumbun Labarai
Hare-haren 'yanta'adda sun kashe gomman sojoji a wurare biyu a Nijar
An zaɓi matasan Nijar 500 domin samun horo a kyauta don koyon sana’o’i a Aljeriya
Fiye da mutum 55,000 daga Sudan sun tsere zuwa gabashin Chadi don gudun hijira
Wasu karin mayakan RSF sun sauya sheka zuwa Rundunar Sojin Sudan bayan sun gamu da 'masifu'
Ana samun ƙaruwar Ƙasashen Yamma masu goyon bayan biyan diyyar cinkin bayi: Ghana
Shugaban Sudan ta Kudu Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar
Zakuna goma sun mutu a wani gandun dabbobi da ke Tanzania
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi da lalata motocin yaƙin RSF
An kama mutum 10 ciki har da jami’an kwastam 4 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Ghana
Rundunar Operation Damissa a Nijar ta lalata maɓoyar mayaƙan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Dosso
Shugaban Nijar Tiani ya sauya wasu ministocinsa
Shugabar Majalisar Dokokin Cabo Verde ta zama shugabar ƙasar ta riƙo
Harin ta'addanci ya yi ajalin sojojin Mali aƙalla 50, da sojojin haya na Rasha biyar
Ƙasashen Afirka biyar sun kawar da yaɗuwar cutar shan inna, amma ba a gama yaƙin ba
Nabil Neghiz ya zama kocin tawagar Mena ta Nijar
Fiye da mutum 7,000 sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Kongo
Shugaban Nijar ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030
Majalisar Sudan ta cire 'yantawayen RSF daga tattaunawar ƙasa
An raba mutane fiye da 4,500 da gidajensu a Darfur ta Kudu da Blue Nile saboda matsalar tsaro