Ƙungiyar gwamnonin Arewa maso-gabashin Nijeriya (NEGF) ta yi shelar shirin kafa kamfanin jiragen sama a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta haɗa mutane a faɗin jihohi shida na yankin.
Wanannan na cikin sanarwar ƙarshen taro da gwamnonin suka fitar a ƙarshen taronsu na 13 a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wata sanarwa da sakataren watsa labaran mataimakin gwamnan jihar Yobe, Hussaini Mai Suleh, ya fitar ta ambato gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, wanda shi ne shugaban ƙungiyar yana cewa an ware naira biliyan 15.8 a matsain kudin haɗin gwiwa na kafa kamfanin jiragen saman na North-East Air Shuttle.
Ya ce ana tsamanin sauran kuɗaɗen haɗin gwiwan kafin ƙarshen shekarar domin kamfanin jiragen saman ya fara aiki.
Zulum ya kuma bayyana cewa ƙungiyar gwamnonin ta jajirce wajen samar da wutar lantarki megawatt goma goma a ko wacce daga cikin jihohi shidan.
Ya bayyana cewa yankin ya samu ci-gaba a fannin tsaro, lamarin da ya danganta ga ƙoƙarin dakarun sojin ƙasar da hukumomin tsaro da kuma juriyar al’ummomi.
Gwamnan ya ce tsaro shi ne ginshiƙin ci-gaba, yana mai ƙarawa da cewa ya kamata yankin ya matsa daga agaji zuwa farfaɗowa kana zuwa wadata mai ɗorewa.
Ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne sake gina al’ummomi masu juriya ta hanyar samar da gidaje da lafiya da damarmaki na arziki ga waɗanda aka raba da gidajensu.
Gwamnonin na neman mataki kan ayyuka 17
Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin arewacin Nijeriya ya ce tsare-tsaren da NEGF zayyana ciki har da sakatrariya da wasu kwamitocin ƙwararru na cikin nasarorin da ta samu.
Gwamnan ya ce gwamnonin sun miƙa wata takardar dabaru mai ayyuka 17 ga Shugaba Bola Tinubu a watan Satumbar shekarar domin ɗaukar mataki na gaggawa.
Ya ce ayyukan sun haɗa da layin dogon Maiduguri da ayyukan neman mai a yankin.
Yahaya ya ce ƙungiyar gwamnonin ta rungumi dabarar amfani da ƙarfin soji da ƙoƙarin yaƙar talauci da rashin ayyukanyi da rashin ilimi da shaye-shaye da kuma haƙar ma’adinai ba biasa ƙa’ida ba.
Gwamnan ya ce dabarun sun kuma haɗa da ƙarfafa raba bayanan sirri tsakanin jihohin da kuma inganta tuntuɓar al’ummomi.





















