Wani jirgin sama na rundunar saman sojin Nijeriya mai lambar NGR 931, ya yi hatsari a ranar Litinin a kusa da sansanin sojin ruwa da ke Igbokoda, Jihar Ondo, a cewar hukumomi.
Ministan Sufurin Jiragen Sama na ƙasar Festus Keyamo ya ce masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun sanar da shi cewa jirgin ya bace daga na’urorin sadarwa da misalin ƙarfe 9:13 na safe, yayin da yake kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas.
Ya ce duk ƙoƙarin tuntubar jirgin ta rediyo bai yi nasara ba, kafin daga bisani aka tabbatar da cewa ya yi hatsari a kusa da sansanin sojin ruwan.
An gano tarkacen jirgin, yayin da ake ci gaba da ayyukan bincike da ceto.
Bayanan farko sun nuna cewa akwai fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin 7 a cikin jirgin, wato mutane 32 gaba ɗaya.
Ministan ya ce ya tattauna da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, tare da tabbatar masa da cikakken haɗin kan ma’aikatar wajen ayyukan bincike da ceto.
Ya ce za a fitar da ƙarin bayani game da hatsarin daga baya.

















