| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Shelar Antalya da Turkiyya ke jagoranta ta haɗa ƙasashe 21 a haɗin kan lumana kan sararin samaniya
Shelar ta haɗa ministoci da 'yanmajalisu da shugabannin hukumomin sararin samaniya bisa amfani na lumana mai ɗorewa da sararin samaniya.
Shelar Antalya da Turkiyya ke jagoranta ta haɗa ƙasashe 21 a haɗin kan lumana kan sararin samaniya
Shekar Antalya da aka mara wa baya a taron IAC, wata muhimmayar alama ce ga haɗin kai na sararin samaniya na duniya . / AA

Wakilai daga ƙasashe 21 sun goyi bayan muhimmiyar shelar Antalya yayin Taron ƙasa da ƙasa na masu ruwa da tsaki a harkar sararin samaniya (IAC) a kudancin Turkiyya, kamar yadda Ministan Masana’ntu da Fasaha na Turkiyya Mehmet Fatih Kacir ya bayyana.

Goyon bayan ya kasance karon farko da aka rungumi shela ta bai-ɗaya a hukumance a taron ministoci da ‘yanmajalisu na IAC, wato MMoP.

Jumullar mutum 32 da suka hallara, da suka haɗa da ministocin gwamnatocin da ‘yanmajalisu da shugabannin hukumomin sararin samaniyyar ƙasashe, sun amince da takardar shekar, wadda ta tabbatar da rawar da Ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta sararin samaniya (IAF) ke takawa wajen haɗin gwiwa a harkar sararin samaniya.

Taron na manyan jami’ai ya haɗa kan wakilai daga ƙasashe 38 domin muhawara kan amfani na lumana da can cikin sararin samaniya, da sabbin tafiye-tafiye na sararin samaniya da tsare-tsaren dokoki da hadin kan ƙasashe masu tasowa da fannin sararin samaniya na duniya.

Tafiyar Turkiyya zuwa duniyar wata a shekarar 2027

Turkiyya tana karɓar baƙuncin karo na 75 na taron daga 5 zuwa 9 ga watan Oktoba, a Antalya, a ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Mansa’antu da Fasaha tare da taron bajekolin kayayykin tsaro da na samaniya na SAHA Istanbul da kuma Hukumar Sararin Tsaron Samaniya na Turkiyya.

Kacir ya bayyana cewa Shelar Antalya ta nuna hangen nesan diflomasiyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan na inganta zaman lafiya ta tattaunawa tsakanin ƙasashe da kuma tuntuɓa ta neman gyara.

"Ci-gaba a sararin samaniya na da ma’ana ne kawai idan ya samar da fa’aidoji masu ma’ana ga mutanen da ke duniya," kamar yadda Kacir ya shaida wa wakilai.

"Tambayar da ke gabanmu ba wai kawai iya ina za mu iya isa ba ne a fannin fasaha, amma ta yaya za mu iya sauya wannan ƙwarewar zuwa ƙarin tsaro da juriya da wadata ga mutanenmu ".

Kacir ya bayyana gaggauta kasuwantar da fannin, yana mai cewa tattalin arziki na fannin sararin samaniya na duniya ya kai wani mataki na tarihi na dala biliyan $686 a shekarar 2025, inda kamfanoni na kasuwa suka kai kimanin kaso 80 cikin 100 na harkokin.

Rage tsadar tura abubuwa sararin samaniya da kuma samuwar ƙananan taurarin ɗan Adam sun rage hana ƙananan kamfanoni shiga fannin sosai.

A cikin gida, fiye da kamfanonin sararin samaniya 300 suna aiki a halin yanzu a sansanonin fasaha na kasuwanci da bincike na Turkiyya, tare da tallafin tsarin kuɗin jari na hukumar BiGG ta Turkiyya da kuma tsarin zuba jari da ya ɗara dala miliyan $750.

Kacir ya tabbatar da cewa Ankara ta kuma fara aiki kan wani wuri na musamman na sansanin fasaha na kasuwanci da bincike kuma tana kan hanyarta ta ƙaddamar da tauraron ɗan’adam na farko da aka haɗa a cikin gida da za a tura duniyar wata a farkon shekarar 2027, wanda ke ɗauke da wani inji na mai amfani da makamashi iri-iri da kuma kashi 80 cikin 100 na ababensa da aka samar daga cikin gida.