| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa — Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya Kashim Shettima
Mataimakin shugaban Nijeriyar Kashim Shettima, wanda ya ce Shugaba Bola Tinubu na “tausayin talaka,” ya ce gwamnatin za ta ƙaddamar da tsare-tsare da ayyuka cikin makonni masu zuwa domin rage raɗaɗin da mutanen ƙasar ke ji.
Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa — Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya Kashin Shettima ya ce gwamnatin ƙasar za ta ƙddamara da shirye-shirye da ayyuka don rage raɗaɗin da 'yan ƙasar ke j

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce matakan tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka sun ceci ƙasar daga durƙushewar tattalin arziki da kuma kare ta daga “wargajewa.”

Shettima ya yi wannan bayanin ne ranar Asabar yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ziyarci Shugaba Tinubu a Legas.

Da yake kare matakan da gwamnatin ta ɗauka kan tattalin arziki, Shettima ya ce kuɗin ajiyar ƙetaren Nijeriya ya gaza dala biliyan $3.9 a lokacin da gwamnatin ta fara aiki, yana mai bayyana tattalin arziƙin a matsayin wanda ke daf da durƙushewa kamar yadda aka samu a Venezuela.

“A lokacin da muka karɓi ragamar mulki, kuɗin ajiyarmu na ƙetare na ƙasa da dala biliyan $3.9 ne wanda bai isa a shigo da mai da shi na wata ɗaya ba,” in ji Shettima.

Ya ce Tinubu na da “jaruntaka da cikakken imanin” ɗaukar matakai irin na cire tallafin mai da kuma daidaita kasuwar canjin kuɗi.

“Cire tallafin mai da daidaita kasuwannin canji wasu matakai ne da ke da tasiri mai yawa.

“Tattalin arzikin na daf da durƙushewa. Ya ceci tattalin arzikin,” in ji mataimakin shugaban ƙasar.

“Ina son ‘yan Nijeriya su gane wannan muhimmiyar gaskiyar. Muna kan hanyarmu ta zuwa Caracas. Ya ceci tattalin arzikin; ya ceci ƙasar daga wargajewa.”

‘Lokacin matsi ba ya tabbata har abada’

Yayin da yake cewa ya san mastin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, mataimakin shugabna ƙasar ya ce gwamnatin na aiwatar da tsare-tsare da ayyuka domin sawƙaƙa nauyin da ke kan ‘yan ƙasar.

“Mun san da wahalar da ‘yan Nijeirya ke sha , amma lokacin masti ba ya tabbata har abada; mutane masu juriya ne ke ɗorewa,” in ji shi.

“Gwamnati za ta ƙddamar da shirye-shirye da ayyuka domin rage raɗaɗin mutane.”

Shettima ya ce gwamnatin za ta ƙaddamar da wasu shirye-shirye ciki har da na jigilar dijital a arewa maso yammacin ƙasar da adaidaita sahu mai amfani da lantarki a arewa maso gabashin ƙasar.

Tinubu yana “tausaya wa talaka,” in ji shi.

“A cikin makonni masu zuwa, za mu ƙaddamar da shirin jigilar dijital a Arewa maso Yamma. Za mu ƙaddamar da adaidaita sahu mai lantarki 10,600 domin rage raɗaɗin mutane a Arewa maso Gabs, da kuma motocin bas 300 da tasi na dijital; duka waɗannan ana yin su ne domin rage raɗaɗin mutanenmu,” in ji shi.

Ganawar a Legas ita ce karon farko da Shugaban ƙasar da mataimakinsa suka haɗu a fili tun bayan Tinubu ya dawo daga hutun da ya je a Turai, kuma lokaci na farko a tun da Shettima ya dawo daga Taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) na 81 a New York.

Tinubu ya shaida wa ƙasar a wani jawabin da ya yi yayin da ƙasar ta cika shekara 66 da samun ‘yancin kai cewa ƙasar na kan hanyar wadata.

Amma manyan jagororin jam’iyyun adawa — Atiku Abubakar na jam’iyyar ADC da Peter Obi na NDC — sun musanta wannan iƙirarin .

yayin da Atiku ya zargi gwamnatin da tsunduma ƙasar cikin matsanancin talauci tun da ta fara aiki a shekarar 2023, Obi ya ce ‘yan Nijeirya na shan wahala a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu sakamakon tsananin yunwa da rashin tsaro.