Mai shigar da ƙara na gwamnatin Madagascar Narindra Rakotoniaina ya ce an kama mutum 11 daga cikin 13, yayin da Kanal Patrick Rakatomamonjy, ɗaya daga cikin manyan waɗanda suka shirya kisan, har yanzu ba a kama shi ba.
Mutane 13, ciki har da wani kwamandan soja, suna fuskantar tuhuma a Madagascar kan wani yunkurin kisan gilla da aka daƙile na kashe Shugaban Kasa Michael Randrianirina.
Mai shigar da ƙara na gwamnatin ƙasar Narindra Rakotoniaina ya ce an kama mutum 11 daga cikin 13, yayin da Kanal Patrick Rakatomamonjy, ɗaya daga cikin manyan waɗanda suka shirya kisan, har yanzu ba a kama shi ba.
Mai shigar da ƙarar ya ambato saƙonnin WhatsApp tsakanin mambobin a matsayin shaidar yunkurin, yana ƙara da cewa an yi bincike a gidajen wasu daga cikin mambobin.
“Wasu daga cikin waɗanda aka kama sun yi iƙirarin cewa kimanin dalar Amurka miliyan 4.8 aka samu a asusun bankinsu an tanade su ne don aiwatar da shirin,” in ji Rakotoniaina, kamar yadda jaridar ƙasar ta L'Express De Madagascar ta ruwaito a ranar Juma'a.
Randrianirina, wanda soja ne mai muƙamin Kanal, ya karbi mukamin a watan Oktoba da ya gabata bayan wata gagarumar zanga-zangar matasa kan ƙarancin wuta da ruwa, wanda ya kai ga kifar da tsohon shugaban kasa Andry Rajoelina har ya gudu daga wannan tsibiri a Tekun Indiya.
A ziyararsa Malabo, Equatorial Guinea mako guda da ya gabata, Randrianirina ya shaida wa ‘yan Madagascar mazauna ƙasashen waje cewa shi da matarsa sun kasance waɗanda aka yi niyyar kamawa sannan an kama waɗanda suka yi yunƙurin hakan.









